SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 08
RUBUTAWA:
Anupama Chopra
FASSARAWA:
Haiman Raees
Sunan Bollywood, wanda ya ƙunshi sunan Bombay da kuma Hollywood, ya daɗe da zama abin cece-kuce. Ƙwararren masanin harshen kamfanin jaridar New York Times William Safire ya bi diddigin wannan kalma in da ya cimma asalinta ga wani marubuci mai suna H. R. F. Keating, shi kuma ya fara amfani da kalmar ne a 1976. Sunan dai an ɗauke shi a matsayin cewa masana'antar fina-finan Hindi suna ƙasa ne da ta Hollywood, kamar dai ace wata ƙaramar masana'antar fim daga wata ƙaramar ƙasa mai tasowa kuma take koyi da fitacciya, ƙayatacciya kuma babbar masana'antar Hollywood.
Jarumai da masu shirya fina-finan Hindi da dama sun nuna rashin amincewa da wannan suna, amma sai 'yan jaridar Indiya suka ɗauki sunan kuma suka tallata shi, an dai fara amfani da kalmar sosai ne a 2001, inda har ma aka sa sunan a cikin Oxford English Dictionary fita ta biyar, daga baya kuma sai ta zama shahararriya a duniya. Bollywood kai tsaye tana nufin Indiya ne. Akwai indiyawa da yawa, ƙasar ita ce ta bakwai a cikin ƙasashen da suka fi girma a duniya. Yayin da kuma take a mataki na biyu a cikin ƙasashen da suka fi yawan mutane a duniya. Ƙasar tana da harsuna guda 23 waɗanda aka tabbatar da su a hukumance, sannan tana da yaruka sama da 2,000. Ƙasa ce mai cike da addinai iri-iri kuma ita ce ƙasa ta uku da ta fi kowacce yawan musulmai a duniya bayan Indonesia da Pakistan.
Indiya ƙasa ce wacce komai nata ya gawurta, saboda ci gaba, da ilimi sun yi kunnen doki da ci baya da kuma jahilci. Zamunna da dama ne ke wanzuwa a lokaci guda. A Mumbai, unguwar matalauta mafi girma za ka iske tazarar su bai fi tafiyar mintuna goma ba zuwa five-star hotel inda ake siyar da jakunan Louis Vuitton kuma farantin abinci ya kai ɗaruruwan daloli. Waɗannan duk suna faruwa a Indiya.
A cikin littafinsa mai suna 'From Midnight to the Millennium', marubuci Shashi Tharoor ya yi wata tambaya, “Menene ke sa maban-bantan mutane su zama ɗaya?"
Amsa ɗaya ita ce Bollywood. Fina-finan Hindi sun zama kamar wani danƙon duniya, suna haɗe kawunan Indiyawa ba tare da banbance jinsi, muhalli, addini ko shekaru ba. Hakan ya ƙunshi harda Indiyawa kimanin miliyan 20 da ke zaune a maban-bantan ƙasashe sama da 110. A gare su, fina-finan Hindi sune mahaɗarsu da ƙasar haihuwarsu. Baƙin hauren zamani na biyu ko na uku kuwa, sukan kalli fina-finan da aka fassara ne saboda ba sa ma jin yaren. Bollywood ita ce hanya ta farko ko mafi girma ta haɗuwa da asalin ƙasar haihuwarsu wacce suka ji labari amma wataƙila ba su taɓa ziyarta ba. A birane irin su New York da London, sukan je kulob ɗin dare domin shagalin Desi nights, in da DJs daga Indiya kan sa musu haɗakar waƙoƙin Bollywood. A taƙaice dai, Bollywood ba wai ƙanwa ce da ake so a kawo kuma ake tsoron kar ta bada kunya ba, fina-finan Hindi suna tashe, don haka Indiya ma na tashe.
Shah Rukh Khan shi ne fuskar sabuwar Indiya mai sheƙi. Akan titunan Indiya, haka za ka iske ana siyar da hotunansa tare da na ababen bauta. An buɗe kushewar wali masu yawa da sunansa. Wa Indiyawa da kuma yawancin masoyan fina-finan Indiya, Shah Rukh ya danne Tom Cruise da Brad Pitt Ko da za a haɗe su wuri guda. Bayan samun shekaru sama da sha biyar da kuma fina-finai sama da hamsin, Shah Rukh ya haye kan Bollywood kamar mai taka matakala. A gidajen ɗaukar shirye-shiryen da ke Mumbai, labarin Shah Rukh, yadda yaron da ya fito daga matsakaicin gidan musulmai daga Delhi ya zama ɗaya daga cikin manyan jaruman babbar masana'antar fina-finan duniya abu ne da ya shiga tarihin da kullum za a dinga labartawa.
A duk lokacin da ya cillar da ragowar karan sigari, haka za ka ga mutane na rububin ɗauka a matsayin tsaraba. Kafar sadarwa kuma, a yanayin da babu zolaya ko cin fuska, sai suka fara yi masa laƙabi da King Khan.
Gidan Shah Rukh, wani babban gini ne mai ɗaukar hankali a Mumbai, wannan gida ya zama wani wajen buɗe ido na musamman. Motocin bas bas kan tsaya a kusa da ginin lokaci bayan lokaci domin sauke baƙi masu son ganin gidan. A yammacin kowace ranar Lahadi kuwa, birnin Mumbai da ke ɗauke da mutane sama da miliyan 18 kan tsaya cak na ɗan wani lokaci saboda mutane da kan tsaya a ƙofar gidan nasa don su ga gilmawarsa. Idan yana gida, wani lokaci yakan fito baranda ya ɗagawa masoyansa hannu a gaisa ya koma ciki.
Sai dai kuma, rayuwar Shah Rukh Khan ba wai kawai ta ƙunshi labarin wasan kwaikwayo bane da fitowa a jaridu da samun nasara. Shi shahararren jarumin fim ne kuma musulmi a ƙasar da 'yan Hindu suka fi yawa, don haka rayuwarsa sai ta zama kamar ƙasa ce da ta samu 'yancin kanta take kuma ƙoƙarin ganin ta yi gogayya da sauran ƙasashen duniya. Labarinsa yana bayyana irin abubuwan da suka taso ne suka saita al'adun Indiya a yau.
©️✍🏻
Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com