Jarumi Shakti Kapoor Ya Bayyana Yanda Asali Yafison Ya Fito a Mugu Kuma Hakan Ana Yaba Masa Amma Wani Lokacin Kwatsam Director Raj Sippy Ya Bashi Dama Ya Fito a Me Barkwanci a Wani Film Satte Pe Satta 1982 Se Ya Tafi Tunanin Akan Me Za a Bashi Wannan Rawar ta Comedy a Film Bayan Ga Abinda Yafiso Amma Be Gaza ba Ya Karɓa Yayi Bayan Nan Shekara Guda Tsakani Watau 1983 Aka Bashi Dama Ya Fito a Me Barkwanci na Wani Film Mawaali Ai Kuwa Anje Ana Aiki Kader Khan Ya Sharara Masa Mari Seda yaje Ƙasa Haka ma Aruna Irani Ta Mareshi Ya Faɗi Ƙasa dai A na 3 ma Aka Mareshi Ya Faɗi Ƙasa Kawai Se Fara Tunanin Shikkenan An Karya Masa Alqadari Domin Yasan Ya Gama Yawo a Bollywood Hakan Yasa Ya Tafi Ya Durƙusa a Gaban Kader Khan Yace Ya Temaka Yayi Masa Booking Zai Koma Gida Ya Haqura da Aikin Nan A Lokacin ma Director na Wannan Film Watau K. Bapaiah Yana Wajen Amma Se Veeru Devgan Shugaban Koya Faɗa na Film ɗin Yace Kar Kayi Karambani Kaje Ko Nawa Za a Mareka Kai dai Kawai Nasara Kake Buƙata da Karɓuwa, Ai Kuwa Bayan Wannan Film Ya fita Ya Samu Yabo Sosai Kuma Film ɗin Karɓu Amma Yayin Da Yayi Wani Film Na Irin Abinda Yafiso Watau Tsayayyan Jarumi Acikin Film Se Akayi Asara Daga Nan Se Ya Hango Cewa Kome Zakayi To Kawai Nasara Itace da Samun Karɓuwa Shine Abinda Kake Buƙata.
#AbbaIndiaDala

