A wannan rana ne ta 20 ga watan December babban ɗan gidan Jaruma "Kareena Kapoor Khan" da jarumi "Saif Ali Khan" wato *Taimur Ali Khan* ya cika shekaru 6 da haihuwa,
Anyi auren Saif da Kareena ne dai a shekarar 2012, bayan shekaru 8 da rabuwar jarumi "Saif Ali Khan" da tsohuwar matar sa kuma mahaifiyar manyan ya'yan sa "Ibrahim Ali Khan" da "Sara Ali Khan" wato jaruma "Amrita Singh" wadda zaman auren nasu yazo ƙarshe a shekarar 2004, bayan shekaru 13 da suka shafe tare,
Al'umma da dama suna yabawa masoyan ma'auratan duba da yadda rayuwar auren nasu take tafiya cikin ban sha'awa da burgewa inda a halin yanzu suka haura shekaru 10 suna tare, sun haifi ya'yan su guda biyu wato "Taimur Ali Khan" da ƙanin sa wato "Jeh",
Yan'uwa da abokan arziki sun wallafa sakon taya murna zuwa ga babban ɗan nasu wato Taimur Ali Khan bisa cika shekaru 6 ɗin da yayi a wannan rana.@AyƘoƘi.