SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 02

SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 02

RUBUTAWA: Anupama Chopra 

FASSARAWA: Haiman Raees 




MEHBOOB KHAN: shi ne wanda ake kira da Cecil B. DeMille of India, Khan shi ne ya shirya fim ɗin Mother India a 1957. Wannan fim shi ne fim ɗin Hindi na farko da ya fara samun gurbin shiga gasar fina-finai ta Oscar.

RAJ KAPOOR: Shi ne babban ɗa ga Prithviraj kuma shi ma babban jarumi ne kuma mai shirya fina-finai.

K. ASIF: Shi ne ya bada umurnin ƙasurgumin shirin soyayyar nan mai suna Mughal-e-Azam. Wanda yana ɗaya daga cikin manyan fina-finan Hindi da ake ji da su. 

SURINDER KAPOOR: ɗaya ne daga cikin mataimakan K. Asif wanda ya ƙulla abota da Meer a Mumbai. Shi ma daga baya ya zama mai ɗaukar nauyin shiri. 

FATIMA: Mahaifiyar Shah Rukh.

SHAHNAZ LALA RUKH: 'Yar uwar Shah Rukh.

MUMTAZ: Babbar jarumar fim ce a 1960s.

RAJESH KHANNA: Shi ne wanda ake kira da Fitaccen jarumi na farko a Hindi cinema. Khanna ya girgiza Indiya a ƙarshen 1960s da farkon 1970s.

JAVED AKHTAR: ƙwararren marubuci ne wanda suka haɗa kai da Salim Khan suka zama Salim-Javed. Su ne suka haifar da sigar fusataccen matashin da jarumi Amitabh Bachchan ya dinga fitowa a yanayinsa a 1970s.

AMRITA SINGH: ƙawar Shah Rukh ce a Delhi wacce ta koma Mumbai kuma ta zama babbar jaruma a 1990s.

GABBAR SINGH: ƙasurgumin ɗan fashin cikin fim ɗin Sholay kenan. Fim ɗin da aka yarda cewa yana daga cikin manyan fina-finan Hindi na gaba ɗaya. 

DHARMENDRA: kyakkywan mutum ne da ya fito daga wani ƙauye da ke Punjab har ya zama babban jarumi a 1960s. Yaransa guda biyu suma sun zama manyan jarumai. 

BROTHER ERIC D’SOUZA: Wani firisti ne a makarantar su Shah Rukh wanda ya zama wani ɓangare na rayuwarsa. 

VIVEK KHUSHALANI: Abokin Shah Rukh ne kuma ɗaya daga cin membobin tawagarsu ta C-Gang. 

RAMAN SHARMA: Abokin Shah Rukh ne kuma ɗaya daga cin membobin tawagarsu ta C-Gang. 

MANI KAUL: shahararren mai bada umarni ne kuma ɗaya daga cikin mutanen farko da suka fara ba Shah Rukh aiki.

BARRY JOHN: Shi ne ya assasa Theater Action Group (TAG) da ke Delhi kuma yake bada umurni. Shi kaɗai ne ya taɓa koyawa Shah Rukh wasan kwaikwayo a duniya. 

BENNY THOMAS: Abokin Shah Rukh ne kuma jarumi a TAG.

DIVYA SETH: Ƙawar Shah Rukh ce kuma memba a TAG, daga baya ta zama shahararriyar jarumar talabijin. 

RITURAJ: Gwarzon TAG kenan a waccan lokaci, shima daga baya ya zamo shahararren jarumin talabijin. 

SANJOY ROY:
Abokin Shah Rukh a Delhi. Sanjoy shi ne executive director na Action Group.

PRADIP KRISHEN: Wani mai shirya fina-finai ne kuma marubuci. Shi ne ya fara ɗaukar Shah Rukh a fim ɗinsa na farko mai suna In Which Annie Gives It Those Ones.

ARUNDHATI ROY: Fitacciyar marubuciya ce kuma 'yar gwagwarmaya wacce ta rubuta kuma ta fito a fim ɗin Annie. A 1997, Roy ta lashe kyautar Man Booker Prize da littafinta na farko mai suna The God of Small Things.

SATYAJIT RAY: fitaccen mai shirya fina-finai ne da ya karɓu kuma ya kafa wasu ginshiƙan tubalan Indian art house cinema da fim ɗinsa Pather Panchali a 1955. 

MRINAL SEN: Ɗaya daga cikin manyan masu shirya fina-finan Indiya da kuma kafa Indian art house move-ment, da ke ɗauke da kambun shirya fim ɗin Bhuvan Shome a 1969.

SHYAM BENEGAL: Fitaccen mai shirya fina-finan Indiya da ke cikin Indian art house movement.

GOVIND NIHALANI: Wani shahararren mai horas da 'yan wasa ne daga Benegal, shi ma yana daga cikin manyan masu bada umurnin'yan art house.

GAURI: Matar Jarumi Shah Rukh 

RAMESH: Mahaifim Gauri. 

TEJINDER TIWARI: Kawun Gauri. 

RAMESH SIPPY: Shi ne wanda ya bada umurnin fim ɗin Sholay.

COLONEL RAJ KAPOOR: Wani soja ne da ya shiga harkar fim da kuma fina-finan gidan talabijin. Shi ne ya bada umurnin shirin Fauji wanda Shah Rukh ya fito a ciki. 

LEKH TANDON: Fitaccen mai bada umurnin fina-finan Indiya ne kuma yana daga cikin waɗanda suka fara ɗaukar Shah Rukh aiki. 

SAVITA: Mahaifiyar Gauri.

NEERU TIWARI: gwaggo/Innar Gauri

VIKRANT CHIBBA: Ɗan uwan Gauri.

KUNDAN SHAH: Ya shahara sosai da shirinsa Jaane Bhi Do Yaaro, Shah ya bayShah Rukh umurni a fina-finan gidan talabijin da kuma wani fim guda ɗaya. 

SAEED MIRZA: Mai bada umurni ne a art house.

AZIZ MIRZA: Ɗan uwa ne ga Saeed, shi ne ya zama kamar uba ga Shah Rukh a Mumbai. Ya kuma bashi umurni a wasu fina-finan da dama.

HAROON MIRZA: Shi kuma ɗa ne ga Aziz, shi ne shaƙiƙin Shah Rukh a lokacin da ya shiga Mumbai.

ASHUTOSH GOWARIKER: Babban jarumi ne da ya fito tare da Shah Rukh a wasu aiyukansa na farko. Daga baya sai ya koma bada umurni, cikin aiyukansa har da Lagaan. 

KETAN MEHTA: Fitaccen mai bada umurni ne da ya bada umurnin fim ɗin Maya Memsaab, maimaicin fim ɗin Madame Bovary, ciki har da Shah Rukh.

AAMIR KHAN: Ɗa ne a wajen babban mai ɗaukar nauyin shiri, Aamir ya fara fim da shekaru huɗu kafinbefore Shah Rukh kuma shima babban jarumi ne.

SALMAN KHAN: Hamshaƙin jarumi ne wanda rayuwarsa ke cike da ƙalubale da kwamacala. Salman, tare da Shah Rukh da Aamir daga baya sun zama Jarumai uku masu suna Khan da ba a taɓa yin kamar su ba a Bollywood sun yi tashe sosai a shekarun 1990s da farkon 2000s.

ANWAR KHAN: Shi ne sakataren Shah Rukh, ya mutu a 2000.

VIVECK VASWANI: Jarumi ne kuma mai ɗaukar nauyin shiri da ya aboci kuma ya tallata Shah Rukh sosai a farkon 1990s.

RAJIV MEHRA: Mai bada umurni ne da suka yi fina-finai biyu da Shah Rukh.

RAJ KANWAR: Shi ne ya bada umurnin shirin Shah Rukh na farko a Bollywood wato Deewana, wanda ya samu nasara daga fitowarsa. 

RAKESH ROSHAN: mahaifi ga Hrithik kuma mai bada umurni da suka yi fim da Shah Rukh.

JUHI CHAWLA: Babbar jaruma ce da suka fito tare da a fina-finai da dama, kuma tana da hannun jari a kamfaninsa na shirya fina-finai.

SUBHASH GHAI: Babban mai Shirya fina-finan Indiya ne da suka yi fina-finai da dama tare da Shah Rukh.

NISHI PREM: fitaccen ɗan Jarida ne da yayi rubututtuka sosai akan Shah Rukh lokacin da ya koma Mumbai. 

Zan ci gaba in sha Allah.

Haiman Raees 
#haimanraees 

Post a Comment

0 Comments