SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 01
RUBUTAWA: Anupama Chopra
FASSARAWA: Haiman Raees
GABATARWAR MAI FASSARA
Tun sanda wannan littafi na King Of Bollywood: Shah Rukh Khan And The Seductive World Of Indian Cinema wanda Marubuciya Anupama Chopra ta rubuta ya shigo hannuna a cikin shekarar 2019, na yi yunƙurin fassara shi zuwa harshen Hausa domin sauran mutane ma'abota kallon fina-finan Indiya su amfana da da tarin bayanan da ke cikinsa. Amma sai Allah bai nufa ba.
To amma sai ga shi cikin yardar Allah yau na fara aikin fassara wannan littafi wanda na sa masa suna SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD. Mai karatu ya kamata ya fahimci cewa, wannan littafi ba aikina bane na ƙashin kaina, don haka kada ka yi min mummunar fahimta in ka ci karo da wani abu wanda kake ganin ya saɓa da tunani, al'ada, addini ko ra'ayinka. Ni aikin da na yi kawai shi ne fassara shi. Ina fata Allah ya amfani wannan rubutu nawa, Allah ya sa ya zama sanadin samun kyakkywar fahimtar da nake fata mutane za su yi wa fina-finan Indiya da jaruman Indiya baki ɗaya. Kuma ina fata Allah ya bani ikon yi wa wannan littafi adalci wajen fassara shi.
Na sadaukar da wannan aiki nawa ga Dukkan masoyan Bollywood, musamman masoyan Shah Rukh Khan.
A sha karatu lafiya.
Jamilu Abdulrahman
(Haiman Raees)
19 October 2020
SHAH RUKH KHAN AND THE SEDUCTIVE WORLD OF INDIAN CINEMA
NA
ANUPAMA CHOPRA
© Haƙƙin Mallaka 2007 Anupama Chopra
First eBook Edition: August 2007 ISBN: 0-446-50893-4 1. Khan, Shah Rukh. 2. Motion picture actors and actresses—India— Biography. I. Title.
Sadaukarwa ga Agni da Zuni, rana da watana, da Vinod.
GABATARWAR MARUBUCIYA
An haifi wannan littafi ne a cikin daminar shekara ta 2003, a lokacin da na fara yi wa Shah Rukh Khan magana kan cewa zan rubuta littafi akansa. Da fari sai da ya jinkirta kuma ya ce ba ya tunanin ya cancanci hakan. Sai na matsa na kuma dage har na shawo kansa. Da fari dai zan so in miƙa godiya ta musamman a gare shi bisa soyayyarsa da goyon bayansa, da kuma haƙurinsa bisa takura irin tawa na tsawon shekaru huɗu, da kuma karramawarsa da abu guda da bashi da shi: lokaci.
Bayan shekaru masu yawa, mutane da dama suna bada gudunmuwa wajen tsaruwar wannan aiki. Zan so in yi godiya ga Karan Johar tare da ma'aikatan Dharma Productions, Fawzan Husain, Rahul Nanda, Joy Datta, Savitha Narayanan, Dinesh Raheja, Jitendra Kothari, Raeshem Nijhon, Rakesh da Preeti Maria, Ram Madhwani, S. Hussain Zaidi, Arun Katiyar, Shankar Aiyar, Sheela Raval, Jitesh Pillai, Kiran Rao, Kishore Lulla, Alice Coehlo da ke Eros, Faizal Sharif, Krishna Desai, Shankra Pillai, Mihiri Kanjirath, Sujoy Das da Rajesh Sharma da ke laburaren India Today, da kuma ma'aikatan Vinod Chopra Films.
Zan so in yi godiya ta musamman ga Nasreen Munni Kabir bisa gudunmuwarta da Leo Mirani bisa gagarumin taimakonsa ta hanyar bincike. Ina miƙa godiyata ga Suketu Mehta bisa haɗa ni da babbar jami'ata Anna Ghosh. Zan so in miƙa godiyata ga Anna bisa ƙarfafa gwiwarta da kuma taimkonta mara iyaka. Ita ce sanadin wanzuwar wannan aikin. Ina kuma miƙa godiyata ga masu tace aikina da ke Warner Books, Devi Pillai da Natalie Kaire.
Ina kuma miƙa godiyata ga mijina Vidhu Vinod Chopra bisa haƙurinsa da takardu a watse cikin ɗakin kwananmu da kuma sautin ƙarar teburin rubutu da misalin 5 a.m., da kuma sanya dukkan lamura zama masu sauƙi da raha irin ta 'yan Punjabi.
Ina godiya ga iyayena, Navin da Kamna Chandra, da 'yar uwata Tanuja. Daga ƙarshe kuma ina miƙa godiyata ga ɗan uwana Vikram Chandra, wanda shi ne makarancina na farko, kuma jagorana.
ABUBUWAN DA KE CIKI
Jarumai A Bisa Tsarin Bayyanarsu
1. Mafarkan Bollywood.
2. Peshawar: Layin Masu Bada Labari.
3. An haifi “Mai Kashe 'Yan Mata”
4. No-Man’s-Land
5. Yakamata ka shiga harkar fina-finai
6. Badaƙala A Panscheel Park
7. Shekarun Talabijin.
8. Rayuwa Bayan Mutuwa.
9. Gagararre
10. Kisan Kai, Ya rubuta.
11. Mai Ƙarfin Zuciya Shi Zai Karɓe Box Office.
12. Abin A Zo A Gani.
13. Brand SRK
14. 'Yan Ta'adda Da Fina-Finai.
15. Mawuyacin Yanayi.
16. Devdas
17. King of Bollywood
18. Manazarta.
JARUMAI A BISA TSARIN BAYYANARSU
AMITABH BACHCHAN: Fitaccen Jarumi mafi juriya da jimiri kenan a Bollywood. A gaba ɗaya shekarun 1970s da na 1980s, shi ake yi wa laƙabi da 'One Man Industry'. Duk da ya haura shekaru 60, ana ci gaba da gwabzawa da shi a box office.
NASREEN MUNNI KABIR: Wani mai shirya fina-finan tarihi ne da ke birnin landan. Tun daga 1986, ya shirya fina-finan tarihi sama da guda tamanin akan masana'antar fina-finan Hindi kuma ya rubuta littattafai da dama akan masana'antar.
DHUNDIRAJ GOVIND PHALKE: Shi ne mutumin da ya fara shirya fim a ƙasar Indiya.
MAHESH BHATT: Fitaccen mai shirya fina-finai masu taɓa zukata ta tare da taɓo ɓangarorin rayuwa da dama waɗanda mafi yawancin labaran fina-finansa sun samo asali ne daga kwamacalar rayuwarsa.
JAWAHARLAL NEHRU: Shi ne firayiminista na farko a Indiya.
PRITHVIRAJ KAPOOR: wani kyakkywan mutum ne daga Peshawar wanda ya zama babban jarumin fim a shekarun 1930s da 1940s. Ya jawo yaɗuwar jarumai da masu shirya fina-finai da dama a sanadiyarsa.
DILIP KUMAR: hamshaƙin jarumi ne da ya shahara matuƙa a shekarun 1950s–1960s, ya shahara matuƙa da taken “Tragedy King.” ƙwarewarsa a fagen iya wasan kwaikwayo ya zama abin koyi ga jaruman da suka zo bayansa, ciki kuwa har da Amitabh Bachchan.
MEER TAJ MOHAMMAD:
Mahaifin jarumi Shah Rukh.
GHULAM MOHAMMAD GAMMA: kawun Shah Rukh.
KHAN ABDUL GHAFFAR KHAN:
Akan yi wa wannan mutumi laƙabi da 'Frontier Gandhi', Khan ya jagoranci harkar yaƙin neman 'yanci a musulunce ba tare da ta'addanci ba kuma yana da alaƙa sosai da Mahatma Gandhi. Mahaifin Shah Rukh da kawunsa duk mabiyansa ne.
KANHAIYA LAL POSWAL: shi ne babban aminin Meer.
DEV ANAND: Jarumi ne kuma mai shirya fina-finai da shahara da salo na musamman a shekarun 1950s–1970s.
BIMAL ROY: Ɗaya ne daga cikin manyan masu bada umurni a Bollywood da ya bada umurnin manyan fina-finai a shekarun 1950s and 1960s.
GURU DUTT: Ɗaya ne daga cikin manya kuma zaƙaƙuran masu shirya fina-finan Indiya da shirya nagartattun fina-finai. Ya kashe kansa a 1964 yana da shekaru 39.
Zan ci gaba in sha Allah.
#haimanraees