FASSARAR WAƘAR AAJ SE TERI
Waƙa: Aaj Se Teri
Fim: Padman
Harshe: Hausa
Shekara: 2017
Sauti: Amit Trivedi
Rubutawa: Kausar Munir
Kamfani: Zee Music Company
Rerawa: Arijit Singh
Fassarawa: Haiman Raees
• Aaj Se Teri Saari Galiyan Meri Ho Gayi
Daga yau dukkan tafarkinki sun zamo nawa.
• Aaj Se Mera Ghar Tera Ho Gaya
Daga yau gidana ya zama gidanki.
• Aaj Se Teri Saari Galiyan Meri Ho Gayi
Daga yau dukkan tafarkinki sun zamo nawa.
• Aaj Se Mera Ghar Tera Ho Gaya
Daga yau gidana ya zama gidanki.
• Aaj Se Meri Saari Khushiyaan Teri Ho Gayi
Daga yau duk wani farinciki nawa ya zamo naki.
• Aaj Se Tera Gham Mera Ho Gaya
Daga yau duk wata damuwa taki ta zamo tawa.
• O Tere Kaandhe Ka Jo Til Hai
Wannan shaidar haihuwar da ke kafaɗar ki.
• O Tere Seene Mein Jo Dil Hai
Zuciyar nan da ke ƙirjinki.
• O Teri Bijli Ka Jo Bill Hai
Takardar kuɗin lantarkinki.
• Aaj Se Mera Ho Gaya
Daga yau, duk sun koma nawa.
• O Mere Khwabon Ka Ambar
Samaniyar mafarkanki.
• O Meri Khushiyon Ka Samandar
Tekun farincikinki.
• O Mere Pin Code Ka Number
Lambar adireshina.
• Aaj Se Tera Ho Gaya
Da ga yau duk sun zama naki.
• Tere Maathe… Tere Maathe Ke Kumkum Ko
Kalar nan da ke tsakiyar gashin kanki.
• Main Tilak Laga Ke Ghoomunga
Nima zan yi kwalliya da shi a kaina in yi yawo a gari.
• Teri Baali Ki Chhun Chhun Ko
Sautin 'yan kunnayenki.
• Main Dil Se Laga Ke Jhoomunga
Zan rungume su a zuciyata.
• Meri Choti Si Bhulon
Duk wasu ƙananan kura-kuraina.
• Ko Tu Nadiya Mein Baha Dena
Don Allah ki bar su su nutse a cikin kogi.
• Tere Joode Ke Phoolon Ko
Fulawoyin da ke jikin adon gashinki.
• Main Apni Shirt Mein Pehnunga
Zan sanya su a jikin riga ta.
• Bas Mere Liye Tu Maalpue Kabhi
Kabhi Bana Dena
Kawai abinda za ki yi shi ne ki dinga haɗa min Maalpua lokaci bayan lokaci.
• Aaj Se Meri Saari Ratiyan Teri Ho Gayi
Daga yau duka darare na sun zama naki.
• Aaj Se Tera Din Mera Ho Gaya
Daga yau duk ranakuna sun zama naki.
• O Tere Kaandhe Ka Jo Til Hai
Wannan shaidar haihuwar da ke kafaɗar ki.
• O Tere Seene Mein Jo Dil Hai
Zuciyar nan da ke ƙirjinki.
• O Teri Bijli Ka Jo Bill Hai
Takardar kuɗin lantarkinki.
• Aaj Se Mera Ho Gaya
Daga yau, duk sun koma nawa.
• O Mere Khwabon Ka Ambar
Samaniyar mafarkanki.
• O Meri Khushiyon Ka Samandar
Tekun farincikinki.
• O Mere Pin Code Ka Number
Lambar adireshina.
• Aaj Se Tera Ho Gaya
Da ga yau duk sun zama naki.
• Tu Maange Sardi Mein Amiya
Da za ki nemi mangwaro a lokacin sanyi.
• Jo Maange Garmi Mein Mungfaliyaan
Da za ki nemi gyaɗa a lokacin zafi.
• Tu Barish Mein Agar Kehde
Ko kuma lokacin ruwan sama ki ce min.
• Ja Mere Liye Tu Dhoop Khila
In je in samar da hasken rana.
• Toh Main Sooraj… Toh Main Sooraj Ko Jhatak Dunga
To zan tayar da rana daga barci.
• Toh Main Saawan Ko Gatak Lunga
Zan shanye ruwan dukka.
• Toh Saare Taaron Sang Chanda
Sannan in haɗa da wata da taurarin gaba ɗaya.
• Main Teri God Mein Rakh Dunga
In ajiye su akan cinyar ki.
• Bas Mere Liye Tu Khil Ke Kabhi Muskura Dena
Kawai ke dai ki ɗan dinga yi min murmushi lokaci bayan lokaci.
• Aaj Se Meri Saari Sadiyan Teri Ho Gayi
Daga yau dukkan zamunna na sun zama naki.
• Aaj Se Tera Pal Mera Ho Gaya
Daga yau, duk lokutan ki sun zama nawa.
• O Tere Kaandhe Ka Jo Til Hai
Wannan shaidar haihuwar da ke kafaɗar ki.
• O Tere Seene Mein Jo Dil Hai
Zuciyar nan da ke ƙirjinki.
• O Teri Bijli Ka Jo Bill Hai
Takardar kuɗin lantarkinki.
• Aaj Se Mera Ho Gaya
Daga yau, duk sun koma nawa.
• O Mere Khwabon Ka Ambar
Samaniyar mafarkanki.
• O Meri Khushiyon Ka Samandar
Tekun farincikinki.
• O Mere Pin Code Ka Number
Lambar adireshina.
• Aaj Se Tera Ho Gaya
Da ga yau duk sun zama naki.
ƘARIN HASKE: Wannan waƙa ce ta soyayya wacce ba ta da bambanci da irin Kalaman da masoyi kan yi wa masoyiyarsa domin ya bayyana soyayyarsa a gareta.
Malpua wani kalan kayan ƙwalama ne mai kama da cake wanda Indiyawa ke yawan mu'amala da shi.
#haimanraees