#SHARHIN_BOX OFFICE Ilimi ne mai zaman kansa 'BABI NA BIYU'
Mutane dayawa sun Gaza fahimtar cewa akwai bambanci a.matakin mizanin farko wurin tantance nasara ko faduwar kafce a Box Office tsakanin films din kudu SOUTH da kuma na Arewaci wato Bollywood..
Girma da yawan makallata da kuma tasirin Bollywood ita kadai daidai yake da masana'sntun kudanci guda4 jimlatan..qaramin misalai2 sune.Bahubaali2 shine mafi amsar kudi a kasuwancin cikin India Wanda yanada Nett Collection na 1,030crs Wanda cikin Alqaluman 510crs daga Bollywood suka fito.sai 520 saga sauran masana'antun kudanci4.Har lau film na2 dayafi karbar kudi a India KGF Chapter2 yanada Nett collection na 859crs wanda 437crs daga Bollywood suka fito.sai masana'antun. Kudu suka bayarda 422crs....idan muka kalla daga wani kusurwa Bollywood a yanxu haka tanada films 5 wadanda suka qetare 500crs a cikinta wato Bahubaali2,Pathaan,Gadar2,Jawan da Stree2...Wanda daga kudanci masana'antun4 Telugu, Tamil,Kannada da Malayalam duk cikinsu babu1 da ita kadai tayi film dinda ya hada 400crs Nett acikinta ita kadai...saidai Collectively sun hada 500crs sau2 akan Bahubaali2 da kuma RRR
Sanan Abin mamaki shine Sunfi Bollywood yiwa kafce manyan kasafin kudi wato Budget...Wanda izuwa yau babu wani kafce da Bollywood ta kashewa 500crs kamar yanda a South akwai 2.0 na Rajnikanth 500crs aka kashe masa,Ga RRR da 550crs sanan ga Kalki da kasafin 600crs..A shekarar nan ta 2024 cikin films da suka fita kafcan da akafi kashewa kudi shine Fighter na Hrithik 250crs..wanda daga kudu a Shekarar nan Bayan Kalki mai 600crs munga kafcaccaki a bays kadan Irinsu GOAT,DEVARA da VETTAIYAN da kasafin Kowanne 300CRORES
Me karatu nasan zakayi mamaki kokuwa ka hasaso a fahimtar Dalilan da suka saka dukda Bollywood girman kasuwanta kwatankwacin na South ita mai4..Sanan kafcaccakin South ke fin na Bollywood samun Babban kasafin kudin hadawa.zakuyi tunanin Dalilai Mabambanta masu karatu.duk wanan dalili nada halaqa da ma'aunin tantance nasarar Film da Faduwa wanda akwai bambanci tsakanin South da Bollywood.
Zan tsaya a nan.A BaBi Na3 zamuyi bayani kan bambancin da sharhi akansa Insha Allah..wanda wasunku sun sani.Ammah dayawa bakuda masaniya