AAGHI AGG 1987 APRIL
KASHI NA BIYU 2
kogon dutsen yayi shiru bakajin matsin komai sai hucin sauran yan mazan jiya ko da yake in kace gun gun yan fashi da makami ma babu wanda zai tuhumeka. kallo daya zaka yi musu kasan cewa wajan bai dace da mutanen arziki ba domin kuwa banajin cikin wadan nan mutanan zaka iya samun mutum guda daya da yataba aikata wani aikin alkhairy a cikinsu bare kuma wani abu wai shi tausayi
koda yake yau an dan sami sauyi kadan dalili kuwa daya daga cikin jagororin wannan tawaga wato mutum na biyu mafi girma a gidan ya turje kuma a yadda ya sheda wa oga kwata kwata a gidan yace shufa daga yau yabar wannan tafiya da take cike da kura kurai hadi da kisan kai kuma wannan bayani nasa ya biyo bayan artabu da akasha dashi a yammacin jiya tare da jamian tsaro a karkashin gada kuma har hakan ya jawo sanadin mutuwar wani likita abin ya bashi tausayi a karon farko saboda acewarsa shine sanadin mutuwar wannan likitan kuma matar shi wannan likitan tazama bazawara dansa kuma yazama maraya
DAINY ya fusata da jin wannan kalamai da suke fita daga bakin babban yaronsa kuma qashin bayan wannan tawaga wato DRAMENDRA
sannan dainy ya yace da dramendra ya kamata kasani idan fa ka dage cewa sai kabar wannan tafiya to da farko dai alumar gari bazasu yafe maka ba sannan gwamnatin india hukuncin kisa ne akan ka gunsu a gefe guda kuma kazama barazana a gunmu domin kuwa hakan yana nufin ka tona mana asiri ka kuwa
san cewa hakan ba abu bane mai yiwuwa ba domin kuwa ni kasani mutan gari suna girmamani a matsayina na dattijon gari dan basu da masaniya cewa nine kan gaba wajan aikata wannan taaddancin akasar nan dadin dadawa kasani yanzu haka ana shirin bani kyautar mutumin da yafi kowanne mutum san zaman lafiya a garin nan to kaga kuwa yin hakan yana nufin rasa kima ta kenan agun alumma to kuwa da haka ta faru gara ace mu da kanmu mu aika dakai garin da baa dawowa ina nufin lahira dainy yace cikun murmushi irin murmushin da soja ya keyiwa abokin gaba alokacin da ya sami damar rutsashi a filin daga
wannan magana ta dainy tayi mutukar bawa daramendra haushi hade da mamaki dramendra ya kalli dainy a fusace sannan yajuya ya kalli sauran yaran dainy sannan cikun izza yace da dainy wato ada kana tunanin kai mutumin kirkine kuma mai kima ko? sannan yayi dariya yace tabbas sau dayawa alumar gari suna wani kuskure dimin kuwa basa iya tantance mutanen kirki dana banza a irin hakane suke zabar irinku a matsayin mutanen kirki a zahiri tabbas kayi kama dasu amma a badini banajin india ta taba yaye babban tsinanne irinka wanda a irinka banajin kataba aikata wani abin alkhary a duniya kuma bana tunanin koda iyalinka zasu iya yima fatan alkhary a bayanka bare kuma wadanda sukasan kai waye
kuma naji kana cewa wai ban isa nabar gidan nan a raye ba to inasan kasani dakai da wadan nan yaran naka kai da ace zaa arama jimian tsaron wannan garin namu wai ku tare min hanya to ina tabbatar ma da cewa da ansami yawaitar zaman makoki a garin nan da banajin fiye da rabinku zaku rayu....
KU BIYONIA CIKIN SHARHIN AAGHI AGG KASHI NA UKU
SHIN DRAMENDRA ZAI FITA DAGA WANNAN KOGON DUTSEN LAFIYA KOKUWA DAINY DA YARANSA ZASU HANA KAMAR YADDA DAINY YAFADA?
MUTTAKA BAGGIO👌🏻