Tsohuwar jarumarnan kuma tsohuwar mawakiya wato VIJAYETA PANDIT ta fito cikin damuwa tana bayyana takaicinta dangane da tsohuwar dangantakarsu da jarumi SHAH RUKH KHAN wanda tace ya kasance abokin mijintane wato mawaki "Aadesh" wanda ya mutu a kwanakin baya, Jarumar ta bayyana cewa jarumi Shah Rukh Khan yayi musu alkawarin ɗaukar nauyin ɗansu har ya zama jarumi a masana'antar Bollywood amma ina! a yanzu dai ko wayarsa ma basa iya samu domin kuwa ko kiransa sukayi layin baya shiga, Dan haka take neman indai jarumin ya samu wannan saƙo nata to suna buƙatar ya taimakesu, Domin kuwa rayuwar gaba ɗaya ta juya musu a halin yanzu.
A wata zantawar da akayi da jarumar kuma bayyanawa manema labarai cewar ita fa a lokacin da ta fara aikin film a yayin da take budurwa bata taba haɗa jiki da wani ɗa namiji ba sai akan jarumin nan wato KUMAR GAURAV wanda dashi ne ta fara yin film ɗin ta na farko mai suna LOVE STORY inda tace a wannan film ɗin ne ta fara yin hakan a cikin wata waka da suka ɗauka a cikinsa wanda daga nan ne kuma soyayya ta shiga tsakaninsu har ma aka fara maganar aure amma kuma mahaifin jarumin wato RAJENDRA KUMAR yace sam bazai yiwu ba ɗan sa ya auri yar talakawa wadda basu da tushen arziki a asalinsu, Inda yace su kam sun yanke shawarar haɗa yayansu aure inda yace ɗansa zai auri yar gidan jarumi RAJ KAPOOR ne mai suna RIMA KAPOOR, Jarumar ta ƙara da cewa tashiga tashin hankali matuƙa bayan raba sun da aka yi, inda tace daga baya ta rungumi kaddara har kuma ta haɗu da ɗan talakawa irin ta wato mawaki AADESH wanda suka share shekaru tare sai gashi kuma yanzu shima ya mutu ya barta, To Ai dama haka rayuwar take, Kowa da irin ƙaddararsa.
Papa Khan