BOMAN IRANI
Wani irin mutum ne tamkar mai sihiri idan aka yi batun buga acting.
Akwai finafinan shi wadanda ya buga acting din da ba zai mantu cikin sauki ba, misali a cikin shirin 3 idiot wanda ya fito a matsayin Viru Sahastrabuddhi, aka VIRUS, yayi playing character din shi yadda ya kamata.
Hakika bani da tantama akan duk character da Boman zai buga, na tabbata zai yi abin da ya dace, Ku tuna da shirin Munnabhai da Main hoon na, ko kuma shirin Lage Raho Munna Bhai.
Hallau a cikin shirin Happy new year ma ya zuba ruwan acting, sai kuma Don 1&2, Pk, dilwale da sauran su
A wasu shekaru baya, jarumi Amitabh bachchan ya taba cewa yana fatan sake hadewa da Boman Irani bayan sun fito tare a cikin shirin Waqt - The Race Against Time, Lakshya da kuma Bhootnath Returns.
Gaskiya Boman na daya daga cikin jaruman da nake so a Bollywood.
#Salafuzzaman

