AAGHI AAG 1987
A FILM DIRECTED BY SHIBU MITRA
STARRING
DHARAMENDRA
SHATRUGHAN SINHA
DANNY DENZONGPA
CHUNKY PENDY
SHAKTI KAPOOR
VINOD MEHRA
and others
A wata yammacin ranar lahadi ne gari yayi dadi babu zafi kwata kwata dalili kuwa yammacin yazo cikin lokacin sanyi
dayawa daga alummar nahiyar kudan cin india suna cikin nishadi sakamakon canji yanayi fa suka samu domin koba komai sun fara fita daga yanayin tsananin zafi
damin kuwa tsananin zafin da yake addabarsu yasa kananan cututtuka suka samarwa kansu gifin zama a nahiyar tasu musamman mata da kananan yara da zaman gida ya aure su
duk inda kaga jamaa za ka gansu cikin nishadi a cikin na hiyar idan ka dauke mutanan wani tsibiri da ake kira kal kuta
awa daya darabi kenan ana musayar wuta tsakanin jamian tsaron kalkuta da wasu gungun yan bidiga kokuma nace yan fashi Allah cikin ikonsa jamian tsaro suka ci karfin yan fashin domin kuwa sun kashe mafiya yawansu
idan ka dauke mutum guda acikin mafasan wato jagoran yan fashin
shima kuma anyi nasarar harbinsa a kafa
shiru ba kajin motsin komai a karkashi katuwar gadar da ake wannan dauku ba dadi sai dai daikun harbin bindiga
kamar wajan yake daukar shiru kimanin minti goma sha biyar babu alamar motsin kowa to a dai dai lokacin ne camera ta dakko hoton karkashin gadar inda shi wannan dan fashi da aka harba rungume da katuwar bindigarsa yana tafanan murku susu saboda zafin harbin da akayi masa cikin tsananin ciwo koda yake ciwon nasa bai hanashi kasancewa cikin shirin kota kwana ba ga duk mai kararren kwanan da ya kawo kai karkashin wannan gada
camera ta sauka daga kan wannan dan fashin sannan ta dakko hotan wani gida da yake nesa da wannan gadar amma yana fuskantar gadar sannu a hankali kuma camera ta dauko hotan wasu mutum biyu ta tagar gidan mace dana miji da kuma dan karamin yaro a kusa dasu
kuma dukkan abinda yake faruwa akan ifan wadan nan maaurata mutumin ya juyo ya kalli matarsa kumanin rabin minti sannan ya dakko farin gilashin sa ya dora akan kyakkyawar fuskarsa ma abociyar annuri yace da matartasa fayal kin fahimci wannan yanayin kuwa?
fayal ta gyada kai a hankali bai bari tabashi amsa ba yaci gaba da cewa wannan mutumin fa da yake karkashin gada yasami rauni kuma yana bukatar agajin gaggawa dan zai iya mutuwa nan da rabin saa idan jininsa ya kare ina ganin ya kamata na taimakeshi .....
matar tasake duban mijin nata a tsorace cikin shakku idon ta ya cicciko da kwalla tace mai gida wannan mumin fa dan fashine baka tunanin yayi maka wani abu kuma kaima sheda ne sun hana alumar wannan gari namu zaman lafiya sannan.......
mutumin ya katse matarsa ta hanyar daga hannu yace da ita ya kamata kisani shi mutumin da yake nagari ne idan yatashi aikata aikin alkhairy baya duba cewa wannan mutumin banza ne kokuwa nagari ne aa zai aikata akhairy ne kawai shikuma mutumin banza idan ya tashi aikata aikn tsiya baya duba mutumin banza kona gari zai aikata abinda yaso ne kawai to kinga anan duk lokacin da akace duk alumma sunzama daya to maanarsa babu wanda zai aikata aikun kwarai a duniya to daga lokacin da duniya tazama haka kuwa zai zama gaba daya mutanen banza ne a cikinta
ya danyi shiru yana maida numfashi sannan ya mike tsaye yafara hada duk wani kayan da zai iya amfani dashi gurin temakon mutumin dayake karkashin gadar wato dan fashin ya sakasu a cikin wata karamar jaka irin wadda likitoci suke amfani da ita a hankali kuma matar shi wannan mutumin ta taso tace nagamsu da bayanan ka mutamin yayi murmushi yace da ita kinsan a kaidar aikinmu na likitanci muna taimakon duk wanda yake da bukatar taimako saidai baa rasa mutanen kawai a cikinmu daga nan ya juya ya shafa kan dan karamin dan nasa yace bari nadawo yau na siyo maka alawar nan daka bani sako
yaron ya daga kai cikin murmushi yace to dady kadawo da wuri
likitan yanufi karkashi gadar da sauri baifi taku goma ya karasa ba shikuma wannan dan fashin saiya jiyo karar takun takalmi sai ya dan leko ta kasan gadar sai ya hangi wani yana matsowa ta kasan gadar kawai saiya ga bakin takalmi da bakin wando irin na jamian tsaro amma bai iya hango rigar dake jikinsa bai tsaya bata lokaci ba sai kawai ya budewa mutumin wuta yakuwa sameshi mutumin ya fadi cikin tsanqnin radadi mara misaltuwa
yana faduwa sai dan fashin yaga ashe ba dansanda bane likita ne
dan fashin ya karaso gun mutumin ya tallafo kansa sukayi shiru na wasu daqiqai sannan likitan yace da dan fashin tabbas rayuwa tana tattare da kalubale banyi tsammanin mutum irinka zai aikata alkhari ba domin kuwa ko bakomai ni nazo gunka da kyakkyawar niya saboda harbin da akayi maka naga ba laifi bane dan na temake ka wala alla ta dalilin haka ka tuba kazama mutumin kirki saidai kai kuma munin zuciyarka bata bari na ida temakon ba..
likitan ya dan sarke sakamakon radadin harshashi
sannan ya cigaba da cewa dukda haka baa makara ba kayi tunani rayuwa da mutuwa koba mutuwa akwai tsufa kuma nasan nan gaba duk mai aiki irin naka dole akwai ranar nadana alal misali akwai lokacin da zakazo kana neman tuba amna lkacin yakure kuma
nasani cewa babu wani dan adam da zai ce bayasan tara iyali to koba komai idan ma akayi saa kasami wanda zai baka ya, wanda hakan abune mai mutukar wahala to hakan yana nufin zaka tara zuri,a
to kaga kenan ka zalunci zuri,arka kenan dan kabar musu mummunan tabo...
likitan yasake runtse ido alamun radadin dake addabarsa yabude idonsa a hankali yace ga shawara zan baka daga yau ka ajiye duk wani mugun aiki ka rungumi nasiha kazama mutymin kirki dukda yake ni bazan rayu ba amma ni nayafe maka kuma ga iyalina can ya saga hannunsa na dama ya nuna masa gidan yace ka kulamin dasu....
daga wannan zance bai kara cewa uffan ba rai yayi halinsa duk wannan abun dake faruwa akan idan matar wannan likita cikin tsananin firgici tayo waje aguje wurin da mijinta yake a kwance tana zuwa ta dauki kwalar wannan dan fashin tana zqginsa tana duka cikin tsananin kuka nan ta fadi ta suma
shi me zai faru shi wannan dan fashin zaibi nasihar wqnnan dan fashin kokuwa aa zaici gaba da fashin?
matar wannan likitan me zai faru da ita da danta?
kubiyoni a cikin sharhin AAGHI AGG KASHI NA BIYU
ina kara bawa masu duba sharhina hakurin rashin jina kwana biyu sakamako yau da gobe sai Allah
Akwai yiwuwar dawowa sharhin Aaghi Aag sakamakon shawarwarin dana samu daga wurare daban daban na zaurikan dasuka shafi harkar indian film
MUTTAQA MUSA USMAN BAGGIO👌🏻