Film dn DHOOM Film ne mai dogon zango wanda kamfanin shirya fina-finai na YASH CHOPRA yake shirya shi, Inda a shekarar 2004 ne aka fitar da kashi na farkonsa wanda ke dauke da jarumai irinsu: ABSHEKH, JOHN, UDAY CHOPRA, ESHA DEOL, RIMI SEN, A shekarar 2006 ne kuma aka shirya kashi na biyunsa wanda shi kuma jarumi HRITHIK ROSHAN da ABSHEKH BACHCHN da UDAY CHOPRA da AISHWARYA da kuma BIPASHA suka jagoranceshi, Sai kuma a shekarar 2014 inda kashi na ukunsa ya fita wanda shi kuma yake ɗauke da jarumai irinsu: AMIR KHAN, ABSHEKH, UDAY CHOPRA da KATRINA KAIF, An yita yaɗa jita-jitar cewar za'ayi kashi na hudunsa wanda akai yita kawo sunan jaruman da ake zaton zasu fito a ciki, To A shekaran jiya ne dai kamfanin ya fitar da sanarwar cewar tabbas ta tabbata za'a fara daukar kashi na hudun wannan Film kuma jarumi RAMBIR KAPOOR ne zai ja ragamarasa inda kuma akace a wannan karon fa babu ABSHEKH BACHCHN da UDAY CHOPRA inda za'a maye gurbinsu da wasu jaruman na daban.
Papa Khan