SHARHIN FIM ƊIN RACHA
Racha fim ɗin faɗaIndia ne da aka fitar a cikin shekara ta 2012 cikin harshen Telugu. Wannan shi ne shiri na farko da jarumi Telugu Ajmal Ameer yayi a Telugu.
• Bada Umurni - Sampath Nandi
• Ɗaukar Nauyi - R. B.
N. V. Prasad
Paras Jain
• Rubutawa - Sampath Nandi
Paruchuri Brothers
• Taken Shiri - Mani Sharma
• Horaswa - Sameer Reddy
• Tacewa - Gautham Raju
• Shiryawa - Megaa Super Good Films
• Ranar Fita - 5 April 2012
• Tsayin shiri - Mintuna 144
• Ƙasa - India
• Harshe - Telugu
A lokacin da aka fitar da wannan shiri ya samu yabo sosai. Shirin ya samu shiga guraben gasar Filmfare har guda 4 a bikin gasar na 60 inda ya lashe kyautar ɗaya wato kyautar Best choreography. Haka kuma shirin ya samu shiga guraben gasar 2nd South Indian International Movie Awards har sau biyar, amma bai ci ko ɗaya ba. An fassara wannan shiri zuwa harshen Hausa inda aka sa masa suna Hatsabibi.
Labarin Shirin.
Raj wani ɗan cacar gasa ne da ke zaune a garin Hyderabad tare da iyayensa na riƙo. Watarana sai mariƙinsa ya kwanta rashin lafiya sakamakon ciwon shan giyar da yake yawan yi ta lalata masa hanta. Raj yana buƙatar kuɗaɗe kimanin ₹20 lakhs domin a yi wannan aikin wanda ya zama dole a yi shi cikin wata ɗaya ko kuma tsoho ya mutu.
Ana cikin haka, sai ga abokin adawarsa wato James ya zo masa da wata cacar gasa. James ya ƙalubalanci Raj da ya sa Chaitra ta kware masa a cikin kwanaki talatin. Ita kuwa wannan budurwa, babanta wani mugun ɗan daba ne kuma hamshaƙin ɗan kasuwa da ake kira da Bellary.
Idan har Raj ya lashe wannan gasa kafin 31 December 2011, James zai bashi kuɗin da yake buƙata domin yin wannan aiki. Idan kuma bai yi nasara ba, to zai yi bankwana da cacar gasa baki ɗaya. Saboda tsananin buƙatar kuɗi da yake yi, Raj sai ya karɓi wannan tayi inda ya fara ƙoƙarin shawo kan Chaitra. Ba da jimawa ba kuwa sai Chaitra ta kware masa. Sai dai Bellary ya gano abin da ke tsakaninsu, hakan ta sa ya aika yaransa da nufin su kashe su a daren 31 December. Sai dai Raj da Chaitra sun samu nasarar guduwa inda suka faɗa dajin Srisailam. Daga nan sai Bellary, Minista Baireddanna da kuma ɗansa suka fara farautarsu a cikin wannan daji na Srisailam, James ya taimaka musu sun kuɓuta daga sharrin Bellary, sai dai ya samu mummunan rauni. Bayan ɗan gidan Minista ya sace Chaitra, sai James ya bayyanawa Raj gaskiyar abin da ya faru a baya.
Mahaifin Raj wato Suryanarayana wani kamilin mutum ne da ake girmamawa a garin Rayadurg, to yana da wani aboki attajiri mai suna Ramamurthy wanda shi ne mahaifin Chaitra. Chaitra da Raj dama abokai ne tun suna yara. Shi kuma Bellary, surukin Ramamurthy ne, yayin da ya gano cewa akwai tuwon ƙarfe a ƙarƙashin ƙasar filin Ramamurthy, sai shi da Baireddanna suka shirya makircin yadda za su amfana da wannan dukiya. Su kuma Suryanarayana da Ramamurthy sai suka nuna ƙin amincewarsu. Hakan ya sa su Bellary hallaka ahalinsu baki ɗaya, Raj da Chaitra ne kaɗai suka rayu. Shi ne sai Bellary ya riƙi Chaitra da nufin cewa da zarar ta kai munzalin budurtaka zai kashe ta ya mallake filin.
Ita kuma Chaitra, saboda ta san halin Raj na shiga cacar gasa, shi ne sai ta sa abokinta na yarinta wato James ya sa shi cikin gasar domin kawar da Bellary da kuma Baireddanna. Raj sai ya sha alwashin ɗaukar fansar ran mahaifinsa inda ya kashe Bellary, Baireddanna da kuma ɗansa a Rayadurg. Sannan kuma ya ceci Chaitra tare da raba filayen Ramamurthy wa mutanen ƙauyen bayan ya aure ta.
Jaruman Shirin
• Ram Charan - Raj
• Tamannaah - Chaitra
• Ajmal Ameer - James
• Mukesh Rishi - Bellary
• Dev Gill - Ɗan Baireddanna
• Kota Srinivasa Rao - Baireddanna
• Nassar - Ramamurthy
• R. Parthiepan - Suryanarayana
• Brahmanandam - Dr. Rangeela
• Ali - Papa Rao
• Diksha Panth - Basanthi, Budurwar Papa Rao
• Paruchuri Venkateswara Rao - Mahaifin James
• Jaya Prakash Reddy - S.I Krishna Varm
• Geetha - matar Bellary
• Venu Madhav
• Srinivasa Reddy
• Thagubothu Ramesh - Bobby
• M. S. Narayana - Mariƙin Raj
• Ravi Babu
• Mukhtar Khan - Police Officer
• Krishna Bhagavaan
Fish Venkat - Venkat
• Jhansi
• Chatrapathi Sekhar
• Lisa Haydon - Fitowa ta musamman.
Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com