SHARHIN FIM ƊIN NAAYAK
Naayak (Hausa: Shugaba) fim ɗin faɗa ne daga kudancin ƙasar India wanda aka fitar a cikin shekara ta 2013. An fassara wannan shiri a cikin harshen Hausa inda aka sa masa suna Masheƙi.
MA'AIKATAN SHIRIN
Umurni: V. V. Vinayak
Ɗaukar Nauyi:. DVV Danayya & S. Radha Krishna
Labari/Tsarawa: Akula Siva
Sauti: S. Thaman
Horar Da 'Yan Wasa: Chota K. Naidu
Tacewa: Gautham Raju
Kamfanin da ya shirya: Universal Media
Kamfanin da yaɗa: Errabus Inc.
(United Kingdom & Europe)
Universal Media
(United States)
Ranar Fita: 9 January 2013
Tsawon shirin: mintuna 151
Ƙasa: India
Harshe: Telugu
Kasafi: ₹35 crores
Kasuwanci:
MATASHIYA
Jarumi Ram Charan ya fito a matsayi biyu ne a cikin wannan shiri. Na farko Cherry, injiniyan na'ura da ke zaune a Hyderabad, sai kuma Siddharth Naayak wanda shi kuma matashin shugaba kuma jagoran talakawa ne a Kolkata inda yake yaƙar wani baƙin mugun ɗan siyasa mai suna Rawat. Shirin yana bada labari ne kan yadda Cherry ya taimakawa Siddharth domin yin nasara akan azzalumai. Wannan shi ne shiri na farko da Jarumi Ram Charan ya fara fitowa a matsayi biyu shi kaɗai.
An fara shirya fim ɗin ne a ranar 9 ga watan Nuwambar 2011, yayinda aka fara ɗauka ta farko a ranar 7 ga watan Fabarairun 2012. Mafi yawancin shirin an ɗauke shi ne a garin Hyderabad da Kolkata, yayin da aka ɗauki wasu Waƙoƙi biyu a birnin Dubai, Iceland da kuma Slovenia, Hakan ya sa Naayak ya zama fim ɗin ƙasar India na farko da aka fara ɗauka a Slovenia. An kammala ɗaukar wannan shiri ne a ranar 29 ga watan Disambar 2012. An saki shirin ne a lokacin bikin Makar Sankranti kuma an haska shi a jikin Majigai guda 1589. Fim ɗin ya samu yabo sosai daga masu sharhi da 'yan kallo baki ɗaya, kuma ya taɓuka abin arziƙi a harkar kasuwancinsa.
LABARIN SHIRIN.
Siddharth Naayak ya kashe ƙanin Ministan tsakiya Rawat watau Taxi Seth tare da muƙarrabansa domin ceto mutanensa guda uku. Daga nan sai Rawat ya sa jami'an 'yan sanda da su nemo shi domin a kashe shi.
A can Hyderabad kuma, akwai wani injiyan na'ura mai suna Cherry wanda kamar su ɗaya sak da Siddharth. Watarana sai kawun Cherry watau Jilebi, wanda kuma shi ne Shugaban kamfaninsu na CgTrix ya faɗa wata gagarumar cakwakiya, domin kuwa ya harzuƙa yaran ɗan dabar da ake jin tsoro watau Babji. Cherry dai ya samu damar ceto kawunsa Jilebi daga Babji ta hanyar hila da yaudara, amma a garin haka sai ya kamu da ƙaunar ƙanwar Babji watau Madhu. Bayan Cherry ya ceci wasu yara daga hannun wani ɗan-ta-kife, sai Madhu ta karɓi soyayyarsa. Wannan abu kuma sai ya harzuƙa Babji har ta kai ga ya yanke shawarar kashe Cherry, amma sai ya firgita yayin da ya ga wanda yake tunanin cherry ne ya kashe shugaban 'yan sandan yammacin Bengal gaba ɗaya. Hakan ya sa suka ɗauka cewa Cherry ne yayi Kisan, alhali kuwa Siddharth ne yayi.
Da taimakon Jilebi dai jami'in' yan sanda mai bincike daga CBI su ka tafi baje-kolin Kumbh Mela da ke Haridwar domin su kama Cherry. Rawat na cikin aikata aiyukan bikin al'ada sai wannan Jami'i na CBI ya kama Cherry, a daidai lokacin ne kuma Siddharth ya fito daga cikin ruwan da ke zagaye da wurin ya soki Rawat da mashi mai baki uku sannan kuma ya yi artabu da dogaran Rawat. Amma sai Jami'in 'yan sandan ya kama shi ya tafi da shi, hakan ya wanke Cherry daga dukkan zargi.
Daga baya sai Cherry ya samu cikakken labarin wannan mutum mai kama da shi. Siddharth ya ziyarci gidan yarsa ne a Kolkata domin ci gaba da karatunsa. Yana matuƙar son wannan ya tasa da mijinta da kuma surikarsa watau Nandini. Hasali ma dai Nandini da Siddharth suna son juna har ma an fara maganar aure.
Ana cikin haka, sai surikinsa wanda ya kasance likita ne ya ya gano cewa fa ƙanin Rawat na biyu wato Badvel yana ba wa yara mata ƙanana sha ka fashe yana tirsasa su yin karuwanci. Yayinda ya kai ƙorafi wa 'yan sanda, bai san cewa ɗan sandan abokin Badvel bane. Hakan ya sa Badvel ya sheƙe shi domin ya sanya shi yayi shiru. Siddharth fa sai ya kasa jurewa wannan al'amari, hakan yasa shima ya sheƙe Badvel, wannan ya sa ya zama sananne cikin ƙiftawar ido.
Ba'a daɗe da yin haka ba kuma, sai Siddharth ya ƙwace duk kadarorin Rawat ya rabawa talakawa. Rawat sai ya kashe minista kuma ya laƙa wa Siddharth laifin sannan ya caccake shi da wuƙa kuma ya jefa shi a kogi.
Cikin sati ɗaya Rawat ya haye kujerar sabon minista. Amma bai san cewa Siddharth ya rayu ba kuma har ya fara shirin sheƙe Rawat. Bayan ya kammala karanta labarin Siddharth, sai Cherry ya yanke shawarar taimaka masa. Da shi da Jilebi sai su ka je magarƙamar da aka kulle Siddharth. Bayan ya gabatar da kansa, sai ya bayyanawa Siddharth Shirinsa. Da aka je kotu, sai Siddharth ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da shi. Alƙali sai ya yanke masa hukuncin kisa.
Kwatsam sai Cherry ya antayo kotun inda ya bayyanawa Alƙali cewa shi ne Siddharth Naayak wanda aka yankewa hukunci kuma ba kowa bane face masoyinsa. Shi ma Siddharth sai ya faɗi daidai da abin da ya faɗa. Hakan ya jawo ruɗani a kotu
Alƙali sai ya ce ya bawa cibiyar bincike ta CBI kwanaki goma su binciko masa wanene na gaskiyar. A cikin waɗannan kwanaki ne Siddharth ya samu ya dawo da Madhu, Babji da Jalebi Kolkata.
Kashe gari sai Rawat ya kira Siddharth ya yi masa ƙaryar cewa ya sace wasu 'yan makaranta ya zo ya cece su, amma sai yayi rashin sa'a domin Cherry ya ji maganar don haka sai shi ya riga Siddharth tafiya. A can, Rawat da mutanensa sun yi masa shegen duka. Siddharth shi ma sai ya ce wajen bayan ya samu saƙo daga Rawat inda ya ceci Cherry kuma su ka kashe Rawat. Kotu sai ta kori ƙarar kuma aka wanke Siddharth. A ƙarshe, duka jaruman biyu sun samu damar kasancewa tare da 'yan matan su.
JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SHIRIN
*. Ram Charan - Charan (Cherry)/Siddharth Naayak.
*. Kajal Aggarwal - Madhu.
*. Amala Paul Nandini.
*. Pradeep Rawat - Minista Rawat.
*. Brahmanandam - Jalebi.
*. Rahul Dev - Babji.
*. Jaya Prakash Reddy - kawun Babji
*. Ashish Vidyarthi - CBI
*. Posani Krishna Murali - Shukla Bhai.
*. Dev Gill - Baldev
*. Surekha Vani - Yayar Siddharth
*. Rajiv Kanakala - Surikin Siddharth
*. M. S. Narayana - Mashayin jami'in CBI
*. Raghu Babu - ɗan jagaliyar Babji
*. Anandhi - ƙanwar Raghu Babu
*. Ajaz Khan - Taxi Seth
*. Vineet Kumar - Dassu
* Venu Madhav - Venu
*. Tanikella Bharani - Alƙali
*. Satyam Rajesh - ɗan jagaliya
*. Sudha - maman Cherry
*. Charmee Kaur
WAƘOƘIN SHIRIN.
1. "Laila O Laila"
2. "Kathi Lanti Pilla"
3. "Subhalekha Raasukunna"
4. "Oka Choopuke Padipoya"
5. "Nellorae"
6. "Hey Naayak"
Haiman Raees
08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com
Miyan Bhai Ki Daring
Aaraha Hoon!