WAƘAR PATHAAN
Kudu da Arewa duk ku zo,
Gabas da Yamma sun zo,
Murna ake yi bisa ƙwazo,
Don malmala ta wuce ƙanzo.
Sarkin nan dai ya fito,
Ya wuce harkar 'yan hoto,
Ya zama gwarzo mai ƙoto,
Kambun nasara ya ƙwato,
Ya bar wasu can na yin toto.
Kyankyaso babban ƙwaro,
Yau Pathaan ya fasa taro,
Giwa iyayen Toro,
Tabbas ko ba ki da tsoro,
Ka ba 'yan maza horo.
Jummai gantali ma ta bi,
Wa ke zancen 'yan kinibibi,
KRK ɗan ƙota ma ya bi,
Wa ke batun 'yan Bjp,
Pathaan dai kowa ya bi.
Ko an so ko da ba a so,
Pathaan yau duniya ke so,
Masoya sun wanke shi da soso,
Maƙiya ma yau na wasoso,
Shamharu kai duniya ke so.
Fatattaka dai ta tabbata,
Daga maza har 'yan mata,
Pathaan yau ya gawurta,
Tiger ma ya yo fita,
Wace ta fi a manta.
Zuciyar Bollywood ta doka,
Jinin Bollywood ya motsa,
Mutane sun fito sinima, Kasuwanci yau ya dawo,
Shamharu babban gwaska.
Haiman Raees
#haimanraees #iamsrk #Pathaan
Infohaiman999@gmail.com