SHARHIN FIM DIN HAPPY NEW YEAR
Happy New Year Fim Din India ne wanda aka yi a 2014, Farah Khan Ce ta bada umurnin Fim Din Yayinda Gauri Khan ta dauki nauyin Fim Din a karkashin Kamfanin Red Chillies Entertainment. Fim Din ya tara manya manyan Jaruman india irin su Shah Rukh Khan , Deepika Padukone ,
Abhishek Bachchan , Sonu Sood , Boman Irani , Vivaan Shah da Jackie Shroff . Kamfanin
Yash Raj Films ne ya Rarraba Fim Din a duniya gaba daya. Wannan Fim shi ne na karo na uku da Jarumi Shah Rukh Khan Da Farah Khan suka yi aiki tare tun bayan haduwar su a Fina Finai biyu wato Main Hoon Na (2004) da Om Shanti Om (2007).
An saki wannan Fim ne da bikin Diwali , 24 October 2014 a cikin Harsuna uku Hindi, Tamil Telugu kuma shi ne babban Fim Din da ya fita a wannan shekarar, Fim Din ya samu Yabo da zagi duka amma a karshe dai ya zama daya daga cikin Fina Finan India Wadanda Suka Fi kowane Fim kawo kudi. Sannan
Academy of Motion Picture Arts and Sciences sun saka shi a cikin labararen su domin adana MUHIMMAN BAYANAI.
Chandramohan Manohar Sharma, wanda aka fi sani da Charlie, dan damben kan titi ne wanda yayi shekaru 8 yana shirin daukar fansa akan Charan Grover. Grover, Kasancewar yana da kudi da kuma bakar Zuciya, sai ya kalawa baban Charlie wato Manohar Sharma Satar Lu'ulu'u Alhalin shi ne ya sace abinsa da kansa, kuma wannan Lu'ulu'u zai kai kimanin Dala Miliyan 15.
A cikin Labarai ne Charlie ya fahimci cewa za'a kai Lu'ulu'u mai darajar Dala Miliyan 300 otal din Atlantis Hotel (wanda kuma shi Grover yana da hannun jari a otal din) Da bikin KIRSIMETI. Charlie sai ya kuduri Aniyar sace wannan Lu'ulu'u domin shima ya kullawa Grover kamar yadda Yayiwa mahaifinsa. Domin ganin ya cimma Burin sa, shi ne ya hada wata Kasaitacciyar Tawaga.
Mutum na farko a cikin Tawagar shi ne tsohon Madatsin Bama Bamai Fi Jagmohan Prakash, wanda aka fi sani da Jag sai dai yana fama da ciwon rashin ji sosai, kuma hakan ya faru ne lokacin yana bakin aiki, in kana son samun matsala da shi to ka fadi maganar banza akan mahaifiyar sa.
Mutum na biyu kuma shi ne Tehmton Irani, wanda aka fi sani da Tammy, masanin sirrin bude akwati, abokin Charlie kuma yana da cutar Farfadiya.
Na uku kuma shi ne Rohan Singh, Matashin Madatsin Na'ura kuma Dan Uwan Charlie. Charlie yayi imani cewa Rohan zai iya datse tsaron da aka sakawa Na'urar Shalimar.
Bayan sun Nazarci Na'urar sosai, sai suka fahimci cewa Na'urar tana dauke da tsaro sosai sai an bude ta da makulli, kuma Makullin zanen dan yatsa ne, kuma na mutum daya wato Vicky da a wajen Grover,saboda haka sai suka nemi taimakon wani mai kama da shi mai suna Nandu Bhide.
Ashe Tammy yana matuqar son wannan zubin Na'urar na Shalimar, kuma shi kadai ne zai iya taba bude ta ba tare da lambobin ta ba wadanda ake sakewa a kullum. Sannan suka gano cewa ita Na'urar Shalimar tana cikin wannan otal na Grover Atlantis hotel dake wani wuri a karkashin kasa kuma yana jo ne ne da daki na musamman mai lambar 9C. Anan ne Charlie ya bayyana musu cewa akwai matsala domin wannan dakin an ajiye shi ne domin bakin 'yan Rawar da zasu yi Gasar rawa ta World Dance Championship (WDC).
Da farko duk sun ki yarda da wannan batun, amma sai Charlie ya sake Shawo kansu tare da Jan Ra'ayin su wajen ganin sun zama kungiyar' yan rawa.
Bayan nan ne asalin labarin ya fito fili : Manohar tsohon injiniyan Kera Na'urorin Tsaro ne. Watarana sai suka hadu da Charan Grover, shi kuma Dila ne na Gwalagwalai a Yankin Ifirikiya, don haka sai ya bashi Kwangilar Sana'anta wata Ma'adana wacce babu mai iya bude ta.
Bayan an kammala Sana'anta Ma'adanar, sai Charan ya bugar da Manohar da kayan maye kuma ya kala masa sharrin sace Gwalagwalan da ke ciki ta hanyar amfani da zanen hannun sa.
Saboda son da suke yi suga sun ci Gasar Rawar nan ta kowane hali, sai suka dinga dauko hayar malaman rawa iri daban daban amma duk a banza. Ganin basu da wata mafita, sai Nandu ya gabatarwa Charlie da Mohini Joshi, wacce ita 'yar Marathi wacce take Cashewa a gidan rawa. Mohini sai ta taimake su wajen koya musu rawa ba tare da ta san hakikanin shirin su ba. Yayinda alaka ta fara kulluwa a tsakanin Mohini da Charlie.
Da karfin tsiya dai sai da suka san yadda suka yi suka lashe Gasar zagayen farko kuma suka zamo tawagar 'yan Rawar da zasu Wakilci India a Gasar rawa ta duniya.
Mutane da yawa sun tsane su, musamman' Yan India saboda rashin iya Rawar su, amma shi Charlie da Mukarrabansa ko a jikin su, Mohini ce kawai take abin da gaske.
A Dubai, sauran Tawagogin 'yan Rawar su ma duk sai suka dinga Nunawa tawagar India Tawariyya, har da Grover, saboda shima ya dauki tawagar India tawagar' yan Asara ne kawai. A zagayen farko sai aka hada su da Tawagar Korea, Charlie har fada suka yi ma da jagoran tawagar Korea. A wasan kusa da karshe, dole tasa wasan su ya tsaya saboda Charlie ya tsaya ceton wani yaro dan tawagar wadanda suke gwabzawa, wannan Abu da ya faru ne fa yasa nan da nan mutane suka koma son su, har ma da 'yan tawagar Korea.
Duk da cewa' yan tawagar Korea sun lashe mataki na karshe da za'a iya kaiwa kafin zagayen karshen Gasar, wannan abun arziki da Charlie yayi yasa alkalan Gasar suka baiwa tawagar India damar taka rawa a zagayen karshe. A cikin dan lokaci sai gashi tawagar India tayi kaurin suna a ko ina.
Mohini kuma a karshe dai taji labarin duk abinda suke shiryawa don haka sai ta Fuskanci Charlie tana mai tuhumar sa. A nan ne Charlie ya sanar musu da cewa Manohar fa baya gidan yari, domin bayan an kama shi, ya nemi a tattauna da lauyan sa a kotu, amma Grover sai ya baiwa Lauyan cin hanci. Shi kuma Manohar ganin bashi da wata Mafita ce yasa ya kashe kanshi. Charlie yace ya boye wannan sirrin ne domin baya so ya Lalata musu tsarin su ko yasa su cikin damuwa.
Sai dai kuma hakan sai ya zama riba wa Charlie domin kuwa hakan yasa duk abokan tafiyar suka sha alwashin taimaka masa Ya dauki fansa, itama Mohini sai ta shiga cikin sahun tafiyar aka ci gaba da tsare tsare.
A DAREN da za'a yi zagayen karshe ne suka Kaddamar da shirin su. Mohini ta jawo Vicky,inda Nandu da Jag suka masa Allurar bacci sannan Nandu ya maye gurbin sa kuma suka samu tambarin hannun sa.
Tammy ya samu damar bude Ma'adanar da kyar bayan ya ciwon Farfadiyar sa ya tashi. To amma sai suka gano cewa ashe kuma akwai wata Ma'adanar a cikin wacce suka bude wacce aka yi da gilashi kuma ita ce Gwalagwalan suke ciki. Tammy sai ya fahimci cewa Manohar ne ya Sana'anta wannan Ma'adanar, don haka ya kamata ace Charlie yasan kalmar sirrin bude ta. Bayan dogon tunani, sai Charlie ya shigar da kalmar sirrin wacce sunan shi ne wato "CHARLIE"
Da suka ga sun yi nasara, sai suka shiga wani jirgin ruwa da nufin su gudu, amma sai Mohini ta ki ta bisu, domin ita a ganin ta Wajibi Ne ta Girmama Kasar India ta hanyar lashe wannan gasa. Rohan shima sai ya bita. Hakan yasa akayi ta cece kuce akan me ya kamata ayi ne.
Shi kuma can Grover duk kanshi yayi zafi ganin an sace Gwalagwalan kuma Vicky ne ya bude kofar wurin. Sai dai ba'a jima ba ya bayyana cewa ai tawagar India ne suka yi Satar. Yayinda aka nemi tawagar India aka rasa, sai Grover ya Hakikance kan cewa Lallai su ne sukayi Satar nan suka gudu da Gwalagwalan.
Yayinda yake kallon Mohini tana taka rawa, sai kuma ga Jag, Tammy, Nandu da Rohan suma sun shigo.
Ana cikin Cashewa sai ga Charlie shima ya shigo fagen da shigar bazata. Daga karshe dai suka lashe Kambun Gasar.
Ganin cewa babu wata hujja da za'a iya tuhumar tawagar India da ita na cewa ita tayi Satar, sai aka kama Vicky da Grover, gab da za'a tafi da su ne Charlie ya Bayyanawa Grover cewa shi Dan Manohar ne
Yayinda tawagar India suka isa filin Jirgi sai Charlie ya zuba Gwalagwalan a cikin abin shan sa wanda masu kula da filin jirgin suka yar a Bola.
Daga baya, bayan sun hau Jirgi, sai Charlie ya bayyana musu cewa ai ya canja Jabun Gwalagwalan kofin Gasar da suka ci ne da asalin Gwalagwalan da suka Sato.
Anan ne Fim Din ya kare inda aka nuno Mohini ta bude gidan koyar da rawa mai suna that "Mohini School of Dance")
JARUMAN FIM DIN
* Shah Rukh Khan = Chandramohan Manohar Sharma / Charlie
* Abhishek Bachchan = Nandu Bhide/Vicky Grover
* Deepika Padukone = Mohini Joshi
* Sonu Sood = Captain Jagmohan Prakash (Jag)
* Boman Irani = Temhton Irani (Tammy)
* Vivaan Shah = Rohan Singh
* Jackie Shroff = Charan Grover
* Varun Pruthi
* Kavi Shastri = Mr. Gupta
* Anupam Kher = Manohar Sharma
* Daisy Irani = Mahaifiyar Tammy
Sarah-Jane Dias = Laila
* Dino Morea
* Kiku Sharda = Saroj Khan
* Prabhu Deva
* Malaika Arora Khan
* Anurag Kashyap
* Vishal Dadlani
* Sajid Khan
* Jason Tham = Shugaban Tawagar Korea
WAKOKIN FIM DIN
1. "India Waale" Vishal Dadlani ,
K.K. ,
Shankar Mahadevan,
Neeti Mohan
2. " Manwa Laage " Arijit Singh,
Shreya Ghoshal
3. "Satakli" Sukhwinder Singh
4. "Lovely" Kanika Kapoor ,
Fateh Doe, Ravindra Upadhyay, Miraya Varma
5. "World Dance Medley" Neeti Mohan, Vishal Dadlani, Sukhwinder Singh, K.K., Shankar Mahadevan,
Shah Rukh Khan
6. "Nonsense Ki Night" Mika Singh
7. "Dance Like A Chammiya" Sunidhi Chauhan , Vishal Dadlani
8. "Sharabi" Manj Musik, Nindy Kaur, Vishal Dadlani,
Shekhar Ravjiani
9. "Indiawaale (Electronic)" Neeti Mohan, Vishal Dadlani, K.K., Shankar Mahadevan
10. "The Heist (Instrumental)" Instrumental
11. "Kamlee" Kanika Kapoor , Ravindra Upadhyay, Miraya Varma,
Fateh Doe,
Dr Zeus
#haimanraees