Ana kiran Shah Rukh Khan Badshah na Bollywood saboda wasu dalilai. King Khan yana son mutane a duk faɗin duniya ba tare da sharadi ba. Jarumin Pathan ya yi nasarar burge mutane tare da sha'awar masu sauraro tare da wasan kwaikwayonsa na ban mamaki da kuma yanayin halayensa. Murmushinsa mai kayatarwa abu ne da mutum ba zai iya Jurewa ba.
Shahararriyar Mujallar na Mai suna "Empire" ta ba da jerin sunayen manyan jarumai 50 All Time kuma Shah Rukh ya zama jarumi Indiya daya tilo da ya shiga jerin. Dama kuma za mu yi mamaki idan Shah Rukh Khan ba ya cikin jerin!
A yayin da ta fitar da jerin sunayen a shafukan sada zumunta, mujallar ta raba jerin manyan jarumai 50 da suka yi fice a kowane lokaci, ciki har da Shah Rukh Khan. Sun rubuta "Jerin daular na manyan 'yan wasan kwaikwayo 50 na kowane lokaci - an bayyana! Kamar yadda aka yi bikin a cikin sabon fitowar mujallar.
YUSUF KHAN DORAYI