Yin ƙarya a harkar kasuwanci abin ban dariya ne – AAMIR KHAN ya magantu akan batun CORPORATE BOOKING.
Halin ɗan Adam ne cewa ‘me yasa zan ce fim ɗina bai tafi ba’; a ganina babu amfani. – Aamir Khan
A kwanakin nan ana ta ce-ce-ku-ce cewa wasu masu kera fina-finai (Producers) suna siyan tikiti da kansu (self-buying), wanda ake kira ‘corporate booking’, domin a nuna kamar fim ɗinsu yana yin kasuwa sosai. Wannan dabara sau da dama ta jawo musu suka, duk da haka har yanzu ana ci gaba da yin ta.
Aamir Khan ya bayyana cewa:
“Lokacin da fim ɗina ya fito, ina gaskata da fitar da ainihin kudaden shiga. Ina gaya wa tawagata kada mu bayar da lambobin ƙarya. A kasuwanci, yin karya abin dariya ne.
Ya ƙara da cewa:
“Za ka iya ruɗar jama’a sau ɗaya ko sau biyu, amma ba za ka iya ruɗar mambobin masana’antar ba. A ƙarshe gaskiya za ta fito fili. A ganina, wannan abu babu amfani.”
A gefe guda, Boney Kapoor ya alakanta lamarin da OTT da satellite, yana cewa a yau yarjejeniyoyin su suna ɗaure da box office. Misali, idan fim ya zarce ₹100 crore, dandamali na OTT ko satellite za su ƙara biyan kuɗi ga masu fim.
#AshiruAamirian
#AshiruBujawa