Aamir Khan ya soki ’yan fim masu amfani da tauraron su ta hanyar da ba daidai ba.
A cikin wata hira, Aamir Khan ya bayyana cewa wasu taurari suna ɗora wa masu kera fim nauyin kuɗaɗen da bai kamata ba – kamar albashin direbobi, masu horarwa a gym, ma’aikatan girki da ma’aikatan gida.
Ya ce: “Ina da mutunci. Me yasa zan bari mai kera fim ya biya direba na ko kuɗin bukatun gida na? Waɗannan ba su da alaƙa da fim. Ni kaina ya kamata in biya su, musamman idan ina samun kuɗi sosai.”
Aamir ya jaddada cewa abin da ya kamata mai kera fim ya ɗauka shi ne kuɗaɗen da suka shafi fim kaɗai – kayan kwalliya, gyaran gashi da tufafi. Sauran bukatun rayuwa suna zama alhakin ɗan wasan kansa.
Ya gargadi cewa irin wannan dabi’a tana lalata masana’antar fim:
“A yau wasu taurari har suna sa a biya musu kuɗin biyan wutar lantarki (TV bills). Wannan mummunar dabi’a ce ga masana’antar.”
#AshiruAamirian
#AshiruBujawa