Deepika Padukone
Deepika Padukone ta kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman Bollywood, tare da nasarori a fina-finai, talla, da aikin agaji. Ta zama alamar ƙarfin mata da haɗin al'adu na duniya .
An haifi Deepika Padukone a ranar 5 ga Janairu, 1986, a Copenhagen, Denmark, ga iyayen Indiya Prakash Padukone (tsohon ɗan wasan badminton na ƙasa) da Ujjala Padukone (ma'aikaciyar yawon shaƙatawa). Ta girma a Bangalore, Indiya, kuma ta yi wasan badminton a matakin ƙasa kafin ta shiga cikin modeling .
Ta halarci makarantar Sophia High School da Mount Carmel College a Bangalore, amma ta daina karatun digiri a fannin ilimin zamantakewa saboda aikin modeling . Ta fara fitowa a cikin tallan Liril soap kuma ta lashe kyautar Model of the Year a 2005. Ta shiga cikin Lakme Fashion Week kuma ta zama jakadiyar nuni da Kingfisher Calendar.
Fim ɗinta na farko ta fito ne a cikin fim ɗin Kannada mai suna Aishwarya (2006), amma ta sami shahara sosai bayan rawar da ta taka a cikin fim ɗin Bollywood Om Shanti Om (2007) tare da Shah Rukh Khan, inda ta lashe Kyautar Filmfare don Mafi kyawun Farkon Fitowa. Sai dai ta yi fice ne a fina-finai irin su Yeh Jawaani Hai Deewani (2013), Chennai Express (2013), da Padmaavat (2018), inda ta nuna rayuwar Rani Padmavati. Jarumar ta lashe kyaututtuka uku na Filmfare Best Actress da fina-finan Goliyon Ki Raasleela Ram-Leela (2013), Piku (2015), da Bajirao Mastani (2015) . Jarumar ta fito a cikin fim ɗin Amurka xXx: Return of Xander Cage (2017) tare da Vin Diesel .
Deepika ta ta fara haɗuwa da Ranveer Singh ne a saitin fara aikin Goliyon Ki Raasleela Ram-Leela (2013), kuma suka yi aure a cikin 2018 a bikin gargajiya a Lake Como, Italiya . A cikin shekarar 2024, ma'auratan sun sanar da cewa suna jiran ɗansu na farko . Ko yarinya ce a ka haifa ko?
Jarumar ita ce ta kafa ƙungiyar The Live Love Laugh Foundation don wayar da kan jama'a game da lafiyar hankali bayan ta sha fama da damuwa a cikin shekarar 2014 . Ta kuma kafa kamfanin kula da fata mai suna 82°E kuma ta zama jakadiyar Louis Vuitton da Cartier .
Fitattun Fina-Finan Deepika Padukone
| 2007 Om Shanti Om
| 2013 | Yeh Jawaani Hai Deewani
| 2015 | Piku
| 2018 | Padmaavat
| 2023 | Pathaan
# haimanraees #bollywood #Fassara #movies