SHARHIN FIM ƊIN CHAK DE! INDIA
Chak De! India Fim ɗin India ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2007 a yaren Hindi. Wannan Fim Kacokan ɗin sa ya ƙunshi abubuwa irin su wasanni, kishin ƙasa, Matantaka, Kacaniyar Ƙasar India Da Pakistan, Ƙabilanci, Wariyar Addinai ɓangaranci ne tare da muhimmancin aiki a tare.
Bada Umurni: Shimit Amin
Ɗaukar Nauyi: Aditya Chopra
Rubuta Labari: Jaideep Sahni
Tsara Labari: Jaideep Sahni
Sauti: Salim-Sulaiman
Jami'in Shiri: Sudeep Chatterjee
Tacewa: Amitabh Shukla
Kamfanin Da Ya Shirya Kuma Ya Yaɗa: Yash Raj Films
Ranar Fita: 10 August 2007
Tsawon Shirin: Mintuna 153
Ƙasa: India
Harshe: Hindi-
English
Kasafi: ₹200 million (daidai da miliyan ₹450 ko dala miliyan US$6.5 kenan a 2018)
Asusun Kasuwanci: ₹1.27 billion (daidai da Biliyan ₹2.9 ko dala miliyan US$41 a 2018)
Chak De! Ya samu lambobin yabo da dama, ciki har da National Film Award for Best Popular Film Providing Wholesome Entertainment. A ranar 30 ga watan Agusta 2007, Academy of Motion Picture Arts and Sciences sun Buƙaci kwafin wannan labari domin ajiye shi a Laburaren Margaret Herrick Library.
LABARIN FIM ƊIN
Chak De! India ya fara ne a birnin Delhi a lokacin da ake buga wasan kofin duniya na ƙwallon Hockey a tsakanin India da Pakistan, inda Ƙasar Pakistan ta ke gaba da 1–0. Yayinda aka yiwa Kyaftin ɗin India Kabir Khan fasha, sai aka bashi bugun daga kai sai mai tsaron gida. Ƙiris ya rage bugun nasa bai shiga ba, hakan ya jawo wa India rashin nasara a wannan wasa.
Bayan nan kuma, sai kafafen yaɗa Labarai suka fara yawo da Hoton Kabir Khan tare da Kyaftin ɗin Pakistan Yayinda suka gaisa. Anan sai suka yiwa salon gaisuwar da suka yi mummunar fahimta, kasancewar sa musulmi, sai aka zarge shi da cewa da gangan yayi abinda yayi don ya tabbatar da nasara wa waccan Ƙasar. Nan fa Kacaniyar Addini da Ƙabilanci ta sa shi dole yabar gidan da suke ciki shi da mahaifiyar sa.
Shekaru bakwai bayan faruwar hakan, sai Mr. Tripathi, wanda shi ne babban mai faɗa aji na ƙungiyar ƙwallon Hockey na Indiya gaba ɗaya ya haɗu da abokin Kabir Khan watau Uttamaji domin su tattauna dangane da ƙungiyar mata masu wakiltar India a Fannin Hockey.
A cewar Tripathi, tawagar bata da gobe, kasancewar iya abinda mata suka fi iyawa na tsawon lokaci kawai shi ne suyi girki kuma su tsaftace gida. Shi kuwa Uttamaji, sai ya faɗa mishi cewa Kabir Khan (wanda babu wanda ya ƙara ganin sa tsawon shekaru bakwai) yana so ya zama Kocin tawagar. Duk da cewa da fari ya nuna rashin amincewar sa, Tripathi ya amince daga baya.
Kabir Khan sai ya tsinci kansa a matsayin mai Jagorantar ƴan mata guda goma sha shida, kowacce kuma daga Mabanbancin waje, kuma kowace tazo da Ƙabilanci da kuma ɓangaranci a cikin zuciyar ta.
Da fari dai akwai Komal Chautala wacce ta fito daga wani ƙauye da ke Haryana, kuma basa shiri da Preeti Sabarwal wacce tazo ita kuma daga Chandigarh; sai kuma wata mara haƙuri mai suna Balbir Kaur daga Punjab, ita kuma Kullum cikin takalar Rani Dispotta take yi da Soimoi Kerketa waɗanda dukkan su sun fito daga wasu ƙauyuka ne da ke Jharkhand. Mary Ralte wacce tazo daga Mizoram da kuma Molly Zimik daga Manipur su kuma sun fuskanci Wariyar launin fata ne da cin zarafi. Ita kuma Kyaftin Vidya Sharma, ya zama dole a gareta ta zaɓi wasan Hockey ko kuma zaɓin ahalin mijinta. Shi kuma saurayin Preeti watau Abhimanyu Singh kasancewa shi ne Mataimakin babban Shugaba a Harkar wasan hockey ta India gaba ɗaya, gani yake akwai matsala tattare da shigarta wannan tawaga.
Kabir Khan sai ya fahimci cewa zai iya kai waɗannan ƴan mata matakin nasara ne kawai idan har ya taimake su suka ajiye banbance-banbancen su a gefe. Hakan yasa a kwanakin sa na farko da fara horar da su ya dinga ajiye ƴan wasan da suka ƙi bin umurnin sa a benci, cikin su kuwa har da Bindiya Naik wacce duk ta fi sauran ƙwarewa. Ganin haka, sai ita kuma Bindiya tayi ta ƙoƙarin tunzura sauran ƴan wasan akan su bijire masa. Yayinda tayi nasara, cikin fushi sai shi kuma ya ajiye aikin, amma sai ya gayyaci ma'aikata da kuma ƴan wasan domin cin abincin bankwana a wani gidan cin abinci na McDonald. A yayin da suke cin abincin ne samarin kan layi suka zolayi Mary; ita kuma Balbir sai ta far musu, hakan ya jawo Rikici a tsakanin ƴan matan da samarin kan layin.
Kabir Khan, ganin cewa wannan shi ne karo na farko da suka fara yin wani aiki tare sai ya hana sauran ma'aikatan shiga tsakanin su. Namiji ɗaya kawai ya dakatar saboda yaga zai daki mace daga baya, inda ya gaya masa cewa babu falalai a wasan hockey. Bayan sun gama wannan Rikici ne sai matan suka roƙi Kabir Khan da ya dawo ya ci gaba da zama Kocin su.
Daga nan kuma sai tawagar ta fara fuskantar Sabbin matsaloli. Da fari dai Tripathi ya hana su zuwa Ƙasar Australia domin wakiltar Indiya a Gasar kofin duniya, hakan ya jawo Kabir Khan ya Buƙaci a haɗa wasa a tsakanin su da tawagar maza masu buga wasan hockey waɗanda ke wakiltar Indiya. Duk da cewa matan ne suka yi rashin nasara, ganin ƙoƙarin da suka yi yasa Tripathi ya bar su suka tafi Ƙasar Australia 🇦🇺.
Ita kuma Bindiya sai ta ɗauki fushi da Kabir akan ya zaɓi Vidya ba ita ba a matsayin Kyaftin ɗin tawagar. Hakan ya jawo musu ci mai zafi inda suka sha kashi akai musu bakwai ba ko ɗaya 7-0 a hannun Australia. Yayinda Kabir ya tuhumi Bindiya dangane da halayyar ta a fili, Bindiya sai ta nemi ta ja Ra'ayin sa domin yayi lalata da ita, amma sai yayi watsi da ita kuma ya dakatar da ita daga buga wasan.
Daga nan sai Kabir ya ci gaba da horar da ƴan matan iya bakin ƙoƙarin sa, hakan ya jawo musu nasara akan England, Spain, South Africa, New Zealand da Argentina. Suna gab da zasu buga wasa da Korea, sai Kabir ya cewa Bindiya ta dawo fili. A nan ne ya tsara musu yadda zasu gudanar da wasan su domin samun nasara. Bindiya ta koma fagen wasa inda da Taimakon Gunjan Lakhani suka samu nasara akan South Korea. Daga nan kuma sai suka sake haɗuwa da Australia a zagayen ƙarshe; inda suka buge su tare da lashe kofin Gasar.
Yayinda tawagar ta dawo gida, an martaba ƴan wasan sosai, Yayinda shi kuma Kabir Khan aka wanke shi tsaf, a Ƙarshe dai sun dawo gidan su na gado sun ci gaba da zama shi da mahaifiyar sa.
JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN SU
Shah Rukh Khan - Kabir Khan/Coach
Vidya Malvade - Vidya Sharma
Anaitha Nair - Aliya
Tanya Abrol - Balbir Kaur
Shilpa Shukla - Bindiya Naik
Arya Menon - Gul Iqbal
Shubhi Mehta - Gunjan Lakhani
Chitrashi Rawat - Komal Chautala
Kimi Laldawla - Mary Ralte
Masochon Zimik - Molly Zimik
Sandia Furtado - Nethra Reddy
Nichola Sequeira - Nichola Sequeira
Sagarika Ghatge - Preeti Sabarwal
Kimberly Miranda - Rachna Prasad
Seema Azmi - Rani Dispotta
Raynia Mascerhanas - Raynia Fernandes
Nisha Nair - Soimoi Kerketa
Anjan Srivastav - Mr. Tripathi
Vibha Chibber - Krishnaji
Javed Khan - Sukhlal
Mohit Chauhan - Uttamaji
Vivan Bhatena - Abimanyu Singh
Nakul Vaid - Rakesh
Joyshree Arora - Mahaifiyar Kabir Khan
Emily White
Waƙoƙin Fim Din Da Mawaƙan su.
1. "Chak De! India - Sukhwinder Singh, Salim–Sulaiman, Marianne D'Cruz
2. "Badal Pe Paaon Hai - Hema Sardesai
3. "Ek Hockey Doongi Rakh Ke - KK, Shahrukh Khan
4. "Bad Bad Girls" - Anushka Manchanda
5. "Maula Mere Le Le Meri Jaan" - Salim Merchant, Krishna Beura
6. "Hockey" (Remix) - Midival Punditz
7. "Sattar Minute" - Shahrukh Khan
#haimanraees