An haifi jaruma ƴar ƙwalisa ranar 2 ga watan September shekarar 1941.
Jarumar da akewa laƙabi da first real female style icon of hindi cinema (Da hausa ƳAR ƘWALISA)
Jarumar ta taka muhimmiyar rawa a tsawon loƙacin da ta safe a masana'antar shirya fina-finai dake ƙasar ta India, inda ta haska cikin mabambantan fina-finai tareda mabambantan jarumai.
Idan mukayi waiwaye wanda masu iya magana ke cewa adon tafiya, zamu ga jarumar cikin jerin fina-finanta kamar....
Mere Hehboob (1963) wanda ta fito da sunan Husna, sai kuma wanda ta fito a matsayin Usha wato Arzoo (1965) sai kuma Meena a Waqt (1965). Waɗannan sune manyan fina-finan da tayi a shekarun 60s wanda suka fito da asalin kyawu da kuma ƙwarewarta.
Hallau na tuna da wani film nata wanda tayi tareda jarumi Sunil Dutt a shekarar 1966 mai suna Mera Saaya, shirin ya zama hit a box office kuma jarumar ta haska a matsayin mutum biyu (double role)
Ana tsaka da bikin Kirsimetin shekarar 2015, labarin mutuwar jarumar ya zagaye duniya, ta mutu tana da shekaru 74 a duniya, ayau tana da shekaru 7 da mutuwa, idan an haɗa daga haihuwarta zuwa yau shekara 81 kenan.
Rayuwar kenan, ku tuna fa itace jarumar ta tafi kowacce jaruma iya kwalliya da ƙwalisa a tarihin masana'antar shirya fina-finai ta ƙasar India, duk iya kwalliyarta, kyawunta da ƙwalisarta kafin yau duk sun gushe, wanda takai ayau ana bikin cikarta shekara 7 da mutuwa. Kafin mutuwarta tsufa ya cimmata ba zaka gane cewa ita bace.
Allah Ubangiji yasa mu dace duniya da lahira.