An haifi wannan jarumi wanda cikakken sunan sa shine "Dharam Singh Deol" a ranar 8 ga watan December na shekarar 1935, a garin Nasrali, yankin Punjab cikin ƙasar India,
Mahaifin sa mai suna "Kewal Kishan Singh Deol" ya kasance makamin makaranta ne, kuma shine shugaban makarantar Secondary ɗin da ɗan nasa ya kammala,
"Dharam Singh Deol" ya bar garin su ya koma "Mumbai" yana da shekaru 25, inda fara samun samun aikin Film ɗin sa na farko a shekarar 1960, ta hannun wani Producer Director mai suna "Arjun Hingorani," wato Film mai suna Dil Bhi Tera Hum Bhi Tere,
Daga nan wannan Director ya zamar wa jarumin Ubangida, inda ya yita fitowa a fina-finai daban-daban amma a matsayin mataimakin jarumi ko jaruma, har dai zuwa 1966, inda ya kafu a masana'antar da wani Film mai suna "Phool Aur Patthar" na wani Director mai suna "O. P. Ralhan" wanda suka fito tare da jaruma "Meena Kumari,"
Bayan kafuwar sa ne fa yayi ta zuba fina-finai cikin nassara inda har yanzu ana damawa dashi, ya fito a fina-finai fiye da 300, ka kaɗan daga fina-finan nashi kamar haka;
~Keemat
~Satyakam
~Naya Zamana
~Do Chor
~Blackmail
~Dharam Veer
~Mohabbat Ki Kasam
~Aaye Din Bahar Ke
~The Burning Train
~Kahani Kismat Ki
~Dharm Aur Qanoon
Yayi fina-finai da mafi yawan jarumai mata na zamanin sa, kamar irin su, Nutan, Saira Banu, Meena Kumari, Rekha, Jaya Prada, Asha Parekh, da kuma matar sa ta biyo wato "Hema Malini" wacce suka yi fina-finai masu yawa tare da ita,
Ga wasu daga cikin jerin fina-finan da Dharmendra da Hema Malini suka fito tare;
~Alibaba Aur 40 Chor
~Raja Jani
~Seeta Aur Geeta
~Sharafat
~Naya Zamana,
~Patthar Aur Payal,
~Tum Haseen Main Jawaan
~Jugnu
~Dost
~Charas
~Maa
~Chacha Bhatija
~Azaad
~Sholay,
Ya auri matar sa ta farko mai suna "Parkash Kaur" a shekarar 1954, inda suka haifi ya'yansu guda huɗu maza 2 "Sunny Deol" da "Bobby Deol" sai kuma mata suma guda 2 wato "Vijeeta da "Ajeeta",
Jarumi"Dharmendra" ya sake auren matar sa ta biyu kuma abokiyar aikin sa wato jaruma "Hema Malini" a shekarar 1980, bayan gwagwarmaya da suka sha kafin yiyuwar wannan aure, inda suka haifi ya'yansu guda biyu duka mata wato "Esha Deol" da kuma "Ahana Deol"
Masoya yan'uwa da abokan arziki har da da manyan jaruman Bollywood irin su jarumi "Ajay Devgan" "Karan Deol," da "Bobby Deol" da sauran su duk sun wallafa saƙon taya murnar karin shekara zuwa ga jarumi Dharmendra.
@AyƘoƘi.