Babban Tauraro Shah Rukh Khan da Yake Ƙoƙarin Fitar da Film ɗin sa Cikin Wata Me Kamawa Yayin da Yake Tallata Gagarumin Shiri Me Taken PATHAN Ya Fadi Yanda Ya Shaho Kan Abokinsa Me Shiryawa Aditya Chopra da Kuma Me Bada Umarni Siddart Anand Domin Yin Wannan Film.
SRK Yace Shekaru Huɗu da Suka Wuce Yayin da Zero Ya Fita Akayi Asara Bayan An Buƙaci Ayi Masa Aiki Tukuru Amma Duk da Haka Mutane Basu Karɓe Shi Hakan Yasa Yaji Ba Daɗi Shiyasa Yace Bari Ya Kara Nutsuwa Ya Huta Sannan Ya Dawo Yazo wa da Ƴan Kallo Irin Abinda Sukeso, Yace Ya faɗawa Aditya da Siddart Akan Suyi Masa Film Na Doke-Doke (Action Film) Sukace Yallabai Zaka Gaji fa Yace Kudai Kuyi Min Duk da Ni Nasan Bazanyi Rigima Kamar Yanda Hrithik da Tiger Suke Ba Amma Zanyi Iya Ƙoƙarina. Jarumin Yace Yanaso Yazo Ba Da irin Salon da Aka Fi Ganinsa ba Watau Zai Sha Ban-ban.
Tun Bayan Da Aka Saki Ƙaramar Talla na Wannan Gagarumin Shirin Wannan Jarumi Ya Fara Samun Yabo Na Yanda Yazo Ba Yanda Ake Tunani ba.
Wannan Film dai Za a Sake 25, ga Watan January 2023. Bayan Shi Akwai Babbar Jaruma Deepika Padukone da John Abraham
#AbbaIndiaDala