SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 11
RUBUTAWA:
Anupama Chopra
FASSARAWA:
Haiman Raees
Peshawar: Layin Masu Bada Labari.
Yankin Qissa Khawani Bazaar da ke Peshawar wuri ne da ke tara jama'a sosai kuma aiyuka da dama suna gudana a wurin. Wuri ne da ke cike da tsoffi da kuma sabbin al'amura. Duka ɓangarori biyu na babbar hanyar yankin cike suke da shaguna waɗanda babu wani takamai-man tsari a yanayin wanzuwarsu. Za ka iske likitoci suna bada magani a kusa da shagunan littattafai, masu siyar da kaya a kusa da masu siyar da nama da dai sauransu.
Kayayyakin gargajiya da makamantansu duk za ka same su maƙil a shagunan. Iskar wurin za ka same ta da nauyi saboda hayaniyar mutane, saboda ƙamshin naman da ake soyawa, biredin da ake gasawa da kuma 'ya'yan itatuwa. Sama da shagunan kuma mazaunin mutane ne iri daban-daban a manne da juna ta yadda idan mutane biyu suka zo wucewa a tare, dole sai dai kowa ya juya ya kalli ɗaya ɓarin.
Tsawon zamunna, yankin Peshawar ya zama dandalin addini, tarihi da kuma cinikayyar jama'a. Birnin yana gabas ne da hanyar Khyber Pass, kuma tun da daɗewa ya zamo matattarar matafiya daga ko'ina. Sarakuna, mahara da 'yan kasuwa duk sun sha wucewa ta Peshawar. A tsakiyar ƙarni na sha tara, kwamishinan Birtaniya a Peshawar ya misalta wannan wuri da cewa nan ne cibiyar yankin Asiya.
Shi wannan wuri ana masa inkiya da Qissa Khawani Bazaar wato “Layin Masu Bada Labari.” Wani abu da zai baka mamaki shi ne; manyan sunayen da suka shahara a fannin harkar fina-finan Indiya da yawansu daga can suka fito. A wani wuri da ake kira da Dahkki Nal Bandi, akwai wani gida wanda Prithviraj Kapoor ya taɓa zama a ciki. Prithviraj ya bar Peshawar a lokacin da yake da shekara 22 a duniya inda ya yi tafiyar kwanaki biyu kafin ya isa garin Mumbai, sai ga shi ya zama ɗaya daga cikin jiggan jaruman da suka shahara a shekarun 1930s da 1940s. Jarumin ya samu karɓuwar da har yanzu ana damawa da ahalinsa a harkar fina-finan Indiya.
Zan ci gaba in sha Allah
©️✍🏻
Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com