SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 10
RUBUTAWA:
Anupama Chopra
FASSARAWA:
Haiman Raees
Ba ka buƙatar sai ka zaɓi ɗayan biyun; kana iya haɗa su duka biyun ba tare da wata matsala ba ko rashin fahimta. Hakan ya sa a cikin DDLJ, Shah Rukh a matsayin Raj, haifaffen ɗan Indiya ne da ke rayuwa a birnin London. Yana shan giya, yana sa rigunan Harley-Davidson, kuma ya yi kama da zubin mutanen Yuropiya sak, amma Raj bai yi amfani da damarsa ba a lokacin da jarumarsa ke cikin maye saboda yana girmama mutuncin 'yar Indiya. Matsayin da jarumi Shah Rukh ya fito a cikin fina-finansa da dama sun ƙara fayyace wannan maganar. Cewa ƙyale-ƙyalen ƙasashen waje ba zai taɓa danne ainahin Indiya ba.
Shah Rukh shi ne zubin ɗan Indiya a wannan zamanin, wanda ya haɗe wayewar kan zamanin duniya da kuma kyawawan al'adu da ɗabi'u irin wanda aka koya daga gida. Shah Rukh ya zama shi ne fuskar ci gaban kasuwancin al'umma baki ɗaya. Yana ɗaya daga cikin jaruman Bollywood na farko da suka shiga harkar tallace-tallace. Abu ne mai wahala a samu wani kaya da Shah Rukh ba zai iya tallatawa ba. Yana tallata komai daga Pepsi-Cola zuwa agogon Tag Heuer. Wannan tallace-tallace da yake ne suka ƙara haɓaka shahararsa har ya zama ɗan kasuwa a ƙashin kansa. Kamar yadda aka faɗa a cikin wata shahararriyar waƙa ta cikin fim ɗin Shri 420 a 1955,
Mera joota hai Japani
Yeh patloon Englistani
Sar pe lal topi Rusi
Phir bhi dil hai Hindustani
Takalmana 'yan Japan ne
Waɗannan wandunan 'yan Birtaniya ne
Hular da ke kaina 'yar Rasha ce
Amma zuciyata 'yar Indiya ce.
Ta yiwu wannan ba komai bane a 1955 face burin zukatan mafi yawancin indiyawa, Amma a yau, wannan shi ne zahirin abin da yake faruwa. Jarumi Shah Rukh Khan, kamar dai Marilyn Monroe, shi ne madubin canji na wannan zamani. Bari ku ji labarinsa.
©️✍🏻
Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com