SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 09
RUBUTAWA:
Anupama Chopra
FASSARAWA:
Haiman Raees
Ana iya fahimtar buwayar Shah Rukh Khan kamar wata ƙasa ce wacce ke ci gaba cikin sauri. A tsakan-kanin shekarun 1990s, ƙasar Indiya ta shiga cikin irin wannan yanayi na sauyi. A shekara ta 1991, ƙasar ta fuskanci matsalar kasa biyan bashin da bankin duniya ke bin ta. Hakan ya sa gwamnatin ƙasar ta kawo hanyoyin da za su bunƙasa arziƙin ƙasar. An rusa kamfanonin ƙasar da dama, aka kuma sabunta wasu sannan aka ba wa kamfanonin ƙasashen waje damar shigowa.
A cikin wannan shekara ce dai kuma, gidajen talabijin ɗin CNN, STAR TV da MTV suka shigo Indiya. Kafin faruwar hakan, matsin da gwamnatin ƙasar ta jawo sakamakon tsare-tsarenta ya sa cin hanci da rashawa ya watsu a ƙasar. Amma bayan da aka samu wannan sauyi, sai abubuwa suka fara canjawa.
Kwatsam sai ga shi hatsi, wandunan jeans, da sauran kamfanoni sun samu a kusan ko'ina. Talabijin, wanda a da ya ƙunshi shirye-shirye gwamnati ne kawai na tsawon awoyi sai ga shi an samu sauyi mai ban mamaki. Hakan ya jawo samuwar sabbin tashoshi waɗanda mutum na iya mallakarsu matuƙar zai iya mallakar talabijin. Tarin zantuka akan siyasa da harkar noma da kiwo sai ga shi an musanya su da ƙayatattun shirye-shirye irin su The Bold and the Beautiful da kuma Baywatch. Kafin ka ce kwabo, yamma da duniya ta shiga matsakaitan gidajen Indiya.
Sai dai kuma, sauye-sauyen da aka samu sun jawo samuwar wasu abubuwan daban, musamman nuna rashin jin daɗi da wata ƙungiya ta Hindu right wing ta nuna. A watan Disambar 1992 ne wasu mabiya addinin Hindu masu tsatstsauran ra'ayi tsuka tarwatsa masallacin Babri Masjid, wanda ya kasance shahararren wurin ibada a arewacin Indiya. Daga nan sai bore kuma ya biyo baya. Birnin Mumbai, wanda ake ganin shi ne babban birni kuma mai ɗauke da mutane iri daban-daban sai ga shi ya watse a sanadiyar bore har sau biyu. A cewa wani rahoto da gwamnati ta sa a yi, mutane 900 ne suka mutu, yayin da guda 2,036 kuma suka jikkata. Sannan sama da mutane dubu 50,000 ne suka rasa muhallansu. Ci gaban zamani ya kasa shawo kai ko kashe wutar rikicin addinanci, talauci, rashawa da kuma tashe-tashen hankulan da ke ƙasa yana dabo.
Al'ummar da ta tsayu sama da shekaru 5,000 tare da al'adunta sai ga shi yau tana faɗa da zamananci, hakan ya sa ta tambayi kanta: me zama ɗan Indiya yake nufi? Shah Rukh Khan ya samar da wata amsa mai sauƙin gaske ga wannan tambayar a cikin fina-finansa irin su Dilwale Dulhania Le Jayenge (1995), Dil To Pagal Hai (1997), Kuch Kuch Hota Hai (1998), Kabhi Khushi Kabhie Gham (2001), da kuma Kal Ho Naa Ho (2003). Jarumin ya bayyanawa Indiyawa cewa: zama ɗan Indiya na nufin cewa kana iya haɗe zamanin da al'adun waje guda. Kana iya jin daɗin zamanancin yamma, kuma ka amfanu da tarbiyya da nutsuwa irin na gabashi a lokaci guda.
©️✍🏻
Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com