FASSARAR WAƘAR SAIYAARA
• Waƙa: Saiyaara
• Fim: Saiyaara
• Harshe - Hindi = Hausa
• Shekarar Fita - 2025
• Sauti - Tanish Bagchi, Arslan Nizami & Faheem Abdallah
• Rubutawa - Irshad Kamil
• Kamfani - Yashraj Music
• Rerawa - Faheem Abdallah
• Fassarawa - Haiman Raees
•Tu paas hai mere paas hai aise
Kina kusa tare da ni ta yadda.
• Mera koi ehsaas hai jaise
Kin zamo wani ɓangare nawa.
•Tu paas hai mere paas hai aise
Kina kusa tare da ni ta yadda.
• Mera koi ehsaas hai jaise
Kin zamo wani ɓangare nawa.
• Haaye main mar hi jaaun, joh tujhko na paaun
Mutuwa zan yi in har ban same ki ba.
• Baaton mein teri main raatein bitaun
Ina tafiyar da dararena ne a cikin kalamanki.
• Hothon pe lamha-lamha hai naam tera haaye
Sunanki na maƙale a laɓɓana koyaushe.
• Tujhko hi gaaun main, tujhko pukaarun
Ke kaɗai nake yi wa waƙa, ke kaɗai nake kira.
• Saiyaara tu toh badla nahi hai
Ya ke tauraruwata, ba ki canza ba ko kaɗan.
• Mausam zara sa rootha hua hai
Yanayin ne kawai ya ɗan harzuƙa.
• Saiyaara tu toh badla nahi hai
Ya ke tauraruwata, ba ki canza ba ko kaɗan.
• Mausam zara sa rootha hua hai
Yanayin ne kawai ya ɗan harzuƙa.
• Beete lamhon se duniya basa loon
Zan iya gina duniya daga lokutana na baya.
• Main toh tere aansuon ka bana hoon
Na wanzu ne daga hawayenki.
• Meri hansi mein teri sadayein
Muryoyinki na rayuwa a cikin dariyata.
• Teri kahani khud ko sunaun
Labarinki nake karanta wa kaina.
• Yaadon ke taare
Taurarin lokutan baya.
• Yaadon ke taare tootenge kaise
Yaya taurarin lokutan baya za su iya karyewa?
• Mere hai joh woh roothenge kaise
Yaya masoyana za su yi fushi da ni?
• Beete dino ki kholi kitaabein
Na buɗe littattafan lokutanmu na baya.
• Guzre palon ko kaise bhula dein
Yaya ma zan manta lokutanmu da muka rayu tare?
• Haaye main mar hi jaaun, joh tujhko na paaun
Mutuwa zan yi in har ban same ki ba.
• Baaton mein teri main raatein bitaun
Ina tafiyar da dararena ne a cikin kalamanki.
• Hothon pe lamha-lamha hai naam tera haaye
Sunanki na maƙale a laɓɓana koyaushe.
• Tujhko hi gaaun main, tujhko pukaarun
Ke kaɗai nake yi wa waƙa, ke kaɗai nake kira.
• Saiyaara tu toh badla nahi hai
Ya ke tauraruwata, ba ki canza ba ko kaɗan
• Mausam zara sa rootha hua hai
Yanayin ne kawai ya ɗan harzuƙa.
• Saiyaara tu toh badla nahi hai
Ya ke tauraruwata, ba ki canza ba ko kaɗan.
•Mausam zara sa rootha hua hai
Yanayin ne kawai ya ɗan harzuƙa.
• Jis roz hum tum phirse milenge
Ranar duk da muka sake haɗuwa.
• Yeh saari baatein tujhse kahenge
Zan faɗa miki dukkan waɗannan abubuwan.
• Duniya mein chahe ban jaaye joh bhi
Ko da me na zama a duniyar nan.
• Tere bina toh kuch na rahenge
Ba Komai bane ni in babu ke.
• Haaye main mar hi jaaun ... joh tujhko na paaun
Zan mutu in ban same ki ba.
• Joh tujhko na paaun ... main mar hi jaaun
Mutuwa zan yi in har ban same ki ba.
• Hothon pe lamha-lamha hai naam tera haaye
Sunanki na maƙale a laɓɓana koyaushe.
• Tujhko hi gaaun main, tujhko pukaarun
Ke kaɗai nake yi wa waƙa, ke kaɗai nake kira.
Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com
#haimanraees #indiansongs #bollywood #bollywoodmovies#bollywoodNigeria #bollywoodmovies
