FASSARAR WAƘAR SOORAJ HI CHHAON BANKE

FASSARAR WAƘAR SOORAJ HI CHHAON BANKE 

• Waƙa: Sooraj Hi Chhaon Banke

• Fim: Salaar: Part 1 – Ceasefire

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2023

• Sauti - Ravi Basrur

• Rubutawa - Riya Mukherjee

• Kamfani - 

• Rerawa - Menuka Poudel

• Fassarawa - Haiman Raees 

• Sooraj Hi Chhaon Banke Aya Hai Aj Tanke

Rana ta fito yau da izzarta domin ta samar mishi da inuwa. 

• Uska Saya Dhal Banke Sath Na Chhode

Inuwarsa ta bunƙasa zuwa kariya, kuma ba za ta taɓa barinsa ba. 

• Aisi Takat Jiske Age Maut Damm Tode

Shi wanin irin ƙarfi ne da hatta mutuwa ma tsoronsa take yi. 

• Har Ik Lamha Hifazat Zameen Se Hai Falak Tak

Cike yake da kariya tun daga ƙasa har zuwa samaniya a koyaushe. 

• Uski Ankhein Baz Jaise Har Taraf Dekhi

Idanuwansa masu kama da na shaho duba ko'ina suke yi. 

• Hai Akela Fauj Jaisa Var Na Chooke

Shi kaɗai rundunar mayaƙa ce, kuma ba ya kuskure abin harinsa. 

• Jhanjha Jangal Mein, Kasauta Dangal Mein

Shi tamkar guguwa ce a cikin daji, yana barin alamarsa a kowane filin yaƙi. 

• Ek Toofan Ek Garjan Mile To Dharati Hile

Yayin da hadari da guguwa suka gwamutsu, dole ne ƙasa ta yi girgiza. 

• Ek Jwala Ek Andhi Phaile To Jale Phatak Kile

Yayin da garwashi da guguwa suka haɗu, sai su tarwatsa duk wani shinge. 

• Dost Aisa Zindagi Mein Har Kisi Ko Mile, Jaise Sans Tann Ko Mile

Fatan kowa zai samu aboki kamarsa, kamar yadda kowane mutum ya samu numfashi. 

• Woh Rusul Jaise Kabhi Rann Tumul Jaise

Kamar ɗan saƙo, wani lokaci kuma kamar fusataccen barde. 

• Ek Dhar Aur Ek Khanjar Ghat Aisi Kare

Yanka yake yi da addarsa cikin ƙwarewa. 

• Dost Aisa Zindagi Mein Har Kisi Ko Mile, Jaise Sans Tann Ko Mile

Fatan kowa zai samu aboki kamarsa, kamar yadda kowane mutum ya samu numfashi. 

• Sooraj Hi Chhaon Banke Aya Hai Aj Tanke

Rana ta fito yau da izzarta domin ta samar mishi da inuwa. 

• Uska Saya Dhal Banke Sath Na Chhode

Inuwarsa ta bunƙasa zuwa kariya, kuma ba za ta taɓa barinsa ba. 

• Aisi Takat Jiske Age Maut Damm Tode

Shi wanin irin ƙarfi ne da hatta mutuwa ma tsoronsa take yi.

©️✍🏻
 Haiman Raees 
Infohaiman999@gmail.com
07064597965
#haimanraees #bollywood #indiansongs

You can also follow my WhatsApp channel here 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VajRSrvIHphDRDBycp09

Comments