RUBUTAWA:
Anupama Chopra
FASSARAWA:
Haiman Raees
Yayin da Shah Rukh ya bashi sifika domin ya yi magana, Bhavesh sai ya ce, “na yi mafarki kwanaki bakwai da suka gabata cewa zan yi rawa tare da Shah Rukh Khan a Atlanta. Na rantse da Allah. Matata ta ƙi yarda da ni akan haka. Sai ma ta ce, ‘Ka zauce, Bhavesh.’ sai na ce, ‘tabbas zai faru.’” Shah Rukh ya saurare shi a nutse cike da murmushi irin na wanda aka fi so, sai ya ma bashi amsa da cewa, “Na taɓu sosai, amma a matsayinka na gaye kamata yayi ace kana mafarkin mata babu kaya.” Daga nan sai Bhavesh ya ce, “ ya zama dole in yi hakan, kada ka ji ba daɗi.” cikin girmamawa mafi daraja da manyan cikin ahali kaɗai ake yi wa da malaman addini a Indiya, Bhavesh ya sunkuya ya taɓa ƙafafuwan Shah Rukh Khan.
Bhavesh ya shafe kusan mintuna talatin tare da Shah Rukh a fagen suna cashewa. Har ma suka yi rawar wata waƙa daga cikin fim ɗin Devdas. Shah Rukh sai ya tambaye shi ko akwai wani abu na musamman da Bhavesh yake so. To dama zagayowar ranar haihuwar Tejal ya matso, sai Bhavesh ya nemi Shah Rukh da ya yi mata Happy Birthday. Bhavesh kuma hallau ya samu sa hannunsa a waɗannan takardu da ke aljihunsa wa ɗansa Kishan wanda a wannan loton yana ta bacci ma. A ƙarshe, Shah Rukh ya bai wa Bhavesh kyautar kwalbar Johnnie Walker Black Label whiskey da kuma tikitin zuwa ko'ina yake so a duniya.
Waɗannan abubuwan da suka faru a wannan cibiya ta Gwinnett Center ita ce ta sa Bhavesh ya fita daban. Domin ya zamo “mutumin da yayi rawa tare da Shah Rukh Khan.” Bhavesh ya ji cewa an taɓa shi ta wata hanya ta musamman. Ga abinda ya ce, “hakan shi ne abu mafi girma da ya taɓa faruwa da ni a rayuwata bayan aure na da haihuwar ɗa na.”
Indiyawa suna hauka ba kaɗan ba akan fina-finai. India ita ce ƙasar da ta fi kowacce yawan fitar da fim a shekara a duniya. Domin tana fitar da fina-finai a ƙalla 800 a shekara. Daga cikinsu, kusan guda 200 suna fitowa ne daga Mumbai, wacce a da aka sani da Bombay. Suna da zubi iri-iri, wasu 'yan shaf-shaf ne da a cikin kwana ashirin ake gama su cikin kasafi mafi ƙaranci, wasu kuma ka ga manyan aiyuka ne da ke buƙatar jarumai da yawa da kuma kayan ƙawa.
A ƙasar da take fama da talauci, cinkoson mutane da kuma zunzurutun zafi, a kowace rana sama da mutane miliyan 15 ne ke zuwa sinimomi a ƙalla 12,500 su kalli fim. Buƙatar da ake yi wa tikitai ya zarce yadda ake kawowa ta yadda masu kasuwancin bayan fage suka yawaita kamar masu siyar da gurguru. Su kan tsaya a ƙofar sinimomin suna kwarzanta irin tashin da farashin tikitin ya yi saboda ana nema. Wajen haska shirin ma kansa wani lokaci abin mamaki ne. Manyan birane irin su Mumbai da Delhi suna da wajen kallo ƙayatattu na manyan mutane kuma akan kawo gurguru mai madara da sikari sosai. Ƙauyuka kuma hakanan suke haƙuri da rumfuna masu ɗan karen zafi yiyin da 'yan kallon ke zama a ƙasa saboda ƙarancin wajen zama. Amma dai ko ma yaya ne, fim ɗin dai zai zama iri ɗaya ne: zafafan waƙoƙi da rawa wanda a cikin wannan fim za ka samu akwai drama, barkwanci, tashin hankali da faɗa duk a gwamutse. Wani lokaci abun ya burge, wani lokaci kuma ga shi nan dai, ta haka ake haɗa masala.
©️✍🏻
Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com